Akwai yuwuwar FG ta rufe kananan hukumomi 18 a Najeriya (Sunaye)

Akwai yuwuwar FG ta rufe kananan hukumomi 18 a Najeriya (Sunaye)

Akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta sake garkame wasu kananan hukumomi 18 a fadin kasar nan saboda su ke da kashi 60 na masu cutar korona a Najeriya.

Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta kasa, Boss Mustapha, ya bada wannan alamar a tattaunawar da yayi da jaridar The Punch tare da sauran manema labaran gidan gwamnati.

Ya zanta da su ne bayan jagorar da yayi wa sauran mambobin kwamitin don tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.

Mustapha, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, ya ce kananan hukumomin da al'amarin ya shafa za su shiga wani sabon tsarin kulle.

A yayin jaddada cewa kasar nan bata kai kololuwa ba dangane da annobar korona, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an kiyaye duk hanyoyin dakile cutar.

Ya kara da bada tsokaci a kan dalilin da yasa ba a cika mutuwa a kasar nan sakamakon cutar ba. Ya ce kashi 80 na wadanda suka harbu da cutar na da shekaru tsakanin 31 zuwa 40 ne wanda ya kwatanta da masu jini a jika.

Kamar yadda hukumar yaki da cututttuka masu yaduwa ta bayyana, 11 daga cikin kanana hukumomi 20 na Legas ne ka da kaso mafi yawa na masu cutar a jihar.

KU KARANTA: Ba kudi muke bukata ba, budurcinta muke so - Masu garkuwa da mutane ga mahaifin budurwa

Ga kananan hukumomi 20 da suka fi kowanne yawan masu cutar a fadin kasar nan kamar yadda hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta bayyana a watan Yuni:

1 – Lagos – Lagos Mainland LG

2 – Abuja – Abuja Municipal

3 – Lagos – Mushin

4 – Lagos – Eti-Osa

5 – Kano – Tarauni

6 – katsina – Katsina

7 – Lagos – Alimosho

8 – Borno – Maiduguri

9 – Lagos – Kosofe

10 – Jigawa – Dutse

11 – Lagos – Ikeja

12 – Kano – Nassarawa

13 – Lagos – Oshodi/Isolo

14 – Lagos – Apapa

15 – Lagos – Amuwo Odofin

16 – Edo – Oredo

17 – Bauchi – Bauchi

18 – Lagos – Lagos Island

19 – Lagos – Surulere

20 – Ogun – Ado Odo/Ota

A ranar 28 ga watan Yuni, alkalumman NCDC ya bayyana cewa akwai masu cutar har 24,567 da suka harbu da muguwar annobar da ta zama ruwan dare a fadin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel