Yanzu-yanzu: FG ta amince da bude makarantu, ta yanke karin hukunci 2

Yanzu-yanzu: FG ta amince da bude makarantu, ta yanke karin hukunci 2

Gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan. Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwab da za su koma bakin karatun sun hada da:

1. Aji shida na dukkan makarantun firamare.

2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.

Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel