Afrika ta Kudu da kasashen Afrika 16 da suka fi kamuwa da cutar korona

Afrika ta Kudu da kasashen Afrika 16 da suka fi kamuwa da cutar korona

- Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da cewa, cutar korona ta harbi mutum 380,207 a duk nahiyar Afrika

- Hukumar ta ce mutum 9,552 suka mutu sakamakon hatsabibiyar cutar a Afrika

- Kasar Afrika ta Kudu ta fi kowacce kasa nahiyar samun yawan mutanen da cutar ta harba yayin da adadinsu ya kai 138,134

An ruwaito cewa akwai fiye da mutum 380,000 da suka kamu da cutar korona a nahiyar Afrika yayin da aka samu sama da mutum 9,500 da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.

Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta tabbatar, akwai fiye da mutum 181,000 da suka samu waraka bayan kamuwa da cutar a duk nahiyar ta Afrika.

Alkaluman Hukumar ta fitar a ranar Litinin 29 ga watan Yuni, sun tabbatar da cewa, akwai mutum 380,207 da cutar korona ta harba a duk ilahirin nahiyar Afrika.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya; Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya; Tedros Adhanom Ghebreyesus
Asali: Facebook

Taskar bayanai ta hukumar ta nuna cewa, an samu salwantar rayukan mutum 9,552 a nahiyar sakamakon kamuwa da kwayoyin cutar.

Cikin jerin kasashen da cutar ta bulla a nahiyar, Afrika ta Kudu ta fi kowacce kasa yawan mutanen da cutar ta harba.

KARANTA KUMA: Kar a buɗe makarantu tukunna - ASUU ta gargadi gwamnati

A halin yanzu akwai mutum 138,134 da cutar Covid-19 ta harba a kasar Afirka ta Kudu, sai kuma kasar Masar inda mutum 63,932 suka kamu.

An samu adadin mutum 24,567 da cutar ta harba a Najeriya, yayin da kuma aka samu mutum 17,351 da ta harba a kasar Ghana.

Sai kuma kasar Aljeriya inda alkaluma suka tabbatar da kamuwar mutane 13,273, yayin da mutane 897 suka riga mu gidan gaskiya.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba cikin kasashe 17 da suka fi kamuwa a nahiyar Afrika:

  1. Afrika ta Kudu – 138,134
  2. Masar – 63,923
  3. Najeriya- 24,567
  4. Ghana – 17,351
  5. Aljeriya – 13,273
  6. Kamaru – 12,592
  7. Morocco – 11,986
  8. Sudan – 9,258
  9. Cote d'Ivoire – 8,944
  10. Ivory Coast – 8,164
  11. Senegal – 6,586
  12. DR Congo – 6,279
  13. Kenya – 6,070
  14. Habasha – 5,689
  15. Guinea – 5,342
  16. Gabon – 5,209
  17. Djibouti – 4,643

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel