Kwamitin yaki da annobar korona ya sake komawa gaban Buhari da sabbin bayanai

Kwamitin yaki da annobar korona ya sake komawa gaban Buhari da sabbin bayanai

Kwamitin kar ta kwana da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar korona a kasa (PTF) ya sake komawa gaban shugaba Buhari domin gabatar ma sa da sabbin bayanai dangane da yaki da annobar.

A yau, Litinin, aka kawo karshen zango na biyu na sassauta dokar kulle da aka saka tun bayan bullar annobar korona.

Ana saka ran cewa kwamitin zai sanar da sabbin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka bayan kammala ganawa da Buhari.

Ma su gabatar da jawabi ga shugaba Buhari duk lokacin da kwamitin ya ziyarce shi sun hada da shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya (SGF); Boss Mustapha, ministan lafiya; Osagie Ehanire, jagoran kwamitin; Dakta Sani Aliyu, da shugaban hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu.

Kwamitin yaki da annobar korona ya sake komawa gaban Buhari da sabbin bayanai
Kwamitin yaki da annobar korona a gaban Buhari a fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

SGF Mustapha ya bayyana cewa zango na biyu na sassauta dokar kulle saboda annobar cutar korona zai dauki tsawon sati hudu.

A ranar 27 ga watan Afrilu ne shugaba Buhari ya sanar da sassauta dokar kulle na tsawon sati biyar da aka fara sakawa a Abuja, Lagos da Ogun.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya cire takunkumin fuska bayan fitowa daga dakin ganawa da Buhari a Villa (Hoto)

Sassauta dokar a karo na biyu ya fara ne daga ranar 2 ga watan Yuni zuwa karfe 12:00 na daren ranar Litinin, 29 ga wata.

Yayin ganawar kwamitin PTF da shugaba Buhari, gwamnati za ta kirkiri sabbin matakan da za ta dauka bayan duba nasarori ko akasin haka da aka samu bayan sassauta dokar.

A makon jiya ne Boss Mustapha ya bayyana cewa da yana da iko da ya sake saka dokar kulle a fadin Najeriya saboda yadda jama'a suka yi watsi da ka'idoji da shawarwarin masana lafiya a kan matakan kare kai da kiyaye yaduwar annobar korona.

Ana cigaba da samun hauhawar alkaluman mutanen da ke kamuwa da kwayar cutar korona a Najeriya, musamman a cikin makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel