Yaki da ta'addanci: Sarkin Daura ya yabawa dakarun sojin kasa da sauran hukumomin tsaro

Yaki da ta'addanci: Sarkin Daura ya yabawa dakarun sojin kasa da sauran hukumomin tsaro

A kokarin kawo karshen ta'addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma, Babban Hafsan Sojojin kasa, Lt Gen TY Buratai, ya ziyarci fadar sarkin Daura.

A ranar Lahadi ne tawagar Buratai ta ziyarci Mai Martaba Umar Farouk Umar, domin yi masa karin haske kan shirin sauke nauyin da ya rataya a wuyan Bataliyar Sojin da ke Daura na kawo karshen matsalar rashin tsaro a yankin.

Janar Buratai ya sanar da Sarkin cewa, ziyarar aiki ce ta kawo shi garin Daura kuma ya yanke shawarar kawo masa ziyarar ban girma.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban hafsan sojin kasa ya kai wa Bataliyar sojin da ke garin Daura wata ziyara tare da yi musu rangadi na kara kaimi da jajircewa.

Ya bai wa masarautar Daura da kuma al'ummar Najeriya tabbaci da cewa, a yanzu rundunar sojin kasa ta sabunta kafiyarta da kuma jarumtar tunkarar kalubale na rashin tsaro da ya addabi Arewa maso Yamma da kuma kasa baki daya.

Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Asali: Facebook

Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Asali: Facebook

Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Asali: Facebook

Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Buratai ya ziyarci Sarkin Daura
Asali: Facebook

Ya ce ziyararsa tana da nasaba ne da nuna damuwa kan yadda a 'yan kwanakin nan 'yan daban daji suke cin karensu babu babbaka wasu sassan na yankin Arewa maso Yamma musamman jihar Katsina.

Shugaban hafsan sojin yayi amfani da wannan dama ta neman masarautar Daura da dukkanin 'yan Najeriya da su ci gaba da yi musu addu'oi da fatan alheri.

Ya tabbatar wa mai martaba Sarkin cewa, rundunar sojin da sauran hukumomin tsaro suna da ikon shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a yanzu, kuma za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.

A nasa jawabin, Sarkin ya yabawa rundunar sojin kasan dangane da jajircewarta da kuma kokarin da take yi na shawo kan matsalar kalubalen tsaro a Najeriya.

KARANTA KUMA: Kakakin majalisar jihar Bauchi ya musanta karbar guraben aiki a shirin N-Power

Sarkin ya bayyana farin cikinsa da kuma yabawa game da hidimar tsaro da rundunar sojin ta ke yi wa al'ummar Daura da kuma na kasa baki daya.

Kazalika, ya kuma fadakar da dukkan 'yan Najeriya game da hadarin da ke tattare da rikice-rikicen tsaro da ke addabar kasar nan.

Ya yi horo da a yi taka tsantsan kan duk wani lamari da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro.

Ya tunatar da al'umma cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulki ne a lokacin da kasar nan ta ke gab da durkushewa.

A sanadiyar haka ne ya bukaci Buratai da ya ci gaba da dagewa kan kyawawan ayyuka da ya fara ba tare da sauraron duk wasu kalamai daga wasu bangarori ba da za su janye masa hankali daga abin da ya sa gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel