Gwamnatin Tarayya ta sake fitar da sabbin sharuɗa 15 na buɗe wuraren bauta
A fafutikar da gwamnatin Najeriya ke yi na dakile yaduwar cutar korona a kasar, ta sake fidda wasu sabbin sharuɗa da za a kiyaye domin wuraren bauta su ci gaba da kasancewa a buɗe.
Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona PTF, shi ne ya sabunta matakan kariya da suka kunshi sabbin sharuɗa da za a kiyaye a masallatai da majami'u.
Ma'aikatar lafiya ta tarayya, ta sanar da cewa wannan sabbin matakan za su taka muhimmiyar rawar gani wajen dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Asali: Twitter
Ga jerin ka'idodin kariya 17 da aka shata wa masallatai:
- Salloli biyar na yau da kullum da sallar juma'a ne kawai aka ba da izinin gudanarwa a masallatai.
- Kada a haura awa daya wajen gudanar da sallar Juma'a tare da hudubarta
- Tsatace dukkanin harabar masallaci, famfo, marikin kofa, da makunnan fitilu da fanka
- Wajibi ne amfani da takunkumin rufe fuska ga dukkan masallata
- Samar da wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana da kuma abin daukar zafin jiki.
- Ba a son mutane su rika gaisawa da juna, sumbata, ko rungumar juna.
- Sanya alamomin tunatar da mutane a kan yin nesa-nesa da juna.
- Tanadar akwatin jefa sadaka a kowace mashiga ta masallatai.
- Samar da ruwa da kuma wurin yin alwala.
- Sanya alamomin bayar da tazara a kan daɓe ko shimfidar masallatai.
- Kada a rika cudanya wajen amfani da Qur'ani, abin shimfida ko butar alwala.
- Babu taron jama'a gabani ko bayan an kammala ibada.
- A tabbatar da tsaftar makewayi da bandakuna.
- Rufe duk wani saye da sayarwa a harabar masallaci.
- An shawarci tsofaffi masu rauni da ke fama da wasu cututtukan kamar ciwon suga da ciwon zuciya da su rika sallolinsu a gida.
- Makarantun Islamiya, Tahfizu, da Makarantun dare za su ci gaba da kasancewa a rufe
- Ana son iska ta wadata saboda haka dole a bude kofa da tagogi a duk lokacin gudanar da ibada a wuraren bauta.
KARANTA KUMA: Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 24, 000 - NCDC
Ga jerin ka'idodin kariya 17 da aka shata wa cocika:
- A ranar Lahadi kadai za a buɗe coci
- Za a buɗe coci daga karfe 5.00 na safe zuwa 8.00 na dare
- A rika bayar da tazara ta awa daya bayan kowane taron masu bauta
- Tsatace dukkanin harabar coci, kofofi, marikin kofa, da makunnan fitilu da lasifika
- Samar da wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana da kuma abin daukar zafin jiki.
- Wajibi ne amfani da takunkumin rufe fuska ga dukkan masu bauta
- Sanya alamomin tunatar da rashin gaisawa da juna, sumbata, ko rungumar juna.
- Tanadar akwatin jefa sadaka a kowace mashiga ta coci.
- Sanya alamomin bayar da tazara a kan daɓen coci.
- Babu taron jama'a gabani ko bayan an kammala ibada.
- A tabbatar da tsaftar makewayi da bandakuna.
- Rufe duk wani saye da sayarwa a harabar coci.
- An shawarci tsofaffi masu rauni da ke fama da wasu cututtukan kamar ciwon suga da ciwon zuciya da su rika sallolinsu a gida.
- A tabbatar da iska ta wadata a wurin bauta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng