FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m

FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m

- Gwamnatin Amurka tana bincike kan wasu 'yan Najeriya shida da suka aikata laifin zamba ta email wanda miliyoyin daloli ke gudana a cikinsa

- Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka, FBI, a ranar Asabar, 27 ga watan Yuni, ta bayyana sunaye da fuskokin mutane shidan da ta ke nema ruwa a jallo

- FBI ta bukaci jama'a da su taimaka wajen samar da muhimman bayanai da za su kai ga kama wadanda ake zargi

Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka, FBI, ta bukaci taimakon al'umma wajen gano wasu 'yan Najeriya shida da ake zargi da hannu a cikin wata badakalar dala miliyan 6.

FBI cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Asabar 27 ga watan Yuni, ta bayyana sunaye da hotunan mutum shidan da ta ke nema ruwa a jallo.

A sakon da ta FBI ta wallafa, ta sanar da cewa mutanen da ta ke nema ruwa a jallo sun aikata wata zamba da makudan kudi da sun kai dala miliyan shida.

Hukumar ta ce mutanen sun ha'inci 'yan kasuwa ta hanyar sakonnin email wajen aikata wannan mummunar badakala.

FBI fidda sunaye da fuskokin 'yan Najeriya 6 da ta ke nema ruwa a jallo
FBI fidda sunaye da fuskokin 'yan Najeriya 6 da ta ke nema ruwa a jallo
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Sarkin Bachama ya riga mu gidan gaskiya

Daga cikin mutanen 10 da hukumar binciken ta kasar Amurka ke neman a taimaka mata wajen lalubo su, shida sun kasance 'yan Najeriya.

Jerin mutum shidan da suka kasance 'yan kasar nan sun hadar da: Richard Izuchukwu Uzuh, Alex Afolabi Ogunshakin, Felix Osilama Okpoh, Abiola Ayorinde Kayode, Nnamdi Orson Benson da Michael Olorunyomi.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Amurka a ranar Talata, 16 ga Yuni, ta sanar da zargin da ta ke yi wa 'yan Najeriyan shida kan yin amfani da fasahar zamani wajen aikata zamba ta dala miliyan 6 (kusan Naira biliyan 3 da digo 3).

Sanarwar wannan zargi ta fito ne daga bakin sakataren harkokin wajen Amurka, Michael Pompeo.

Dangane da bayanan da shafin yanar gizon ma'aikatar baitulmalin kasar ta bayyana, wadanda suka aikata laifin na zamba, 'yan tsakanin shekaru 32 zuwa 37 ne.

Ana zargin mutanen shida sun yi amfani da fasahar zamani wajen yin kutse kan wasu harkokin kasuwanci na Amurka masu rauni.

Mutanen shida da ake nema a yanzu sun karkatar da dukiyar wadanda abin ya shafa ta hanyar yaudara da yin amfani da wasu bayanan sirri da suka zakulo wajen yashe musu tattalin arziki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng