Shugaban Majalisar Dattawa ya musanta zargin rarrabawa Sanatoci aikin N-Power

Shugaban Majalisar Dattawa ya musanta zargin rarrabawa Sanatoci aikin N-Power

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya musanta rade-radin da ke yaduwa na cewa an bai wa sanatoci gurabe a aikin N-Power da ake shirin daukan matasa a yanzu.

Sanata Lawan cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawunsa, Ola Awoniyi, ya misalta rahotannin a matsayin tatsuniya da shaci fadi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sanata Lawan ya nemi al'umma da su yi watsi da wannan rahotanni masu yaduwa da cewa an ba shi gurabe a aikin shirin N-Power da za a dauki matasa.

Kakakin shugaban majalisar da yayin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar cikin birnin Abuja, ya ce wannan rahotanni da wasu kafofin yada labarai ke yadawa ba wani abu bane face kanzon kurege.

Shugaban Majalisar Dattawa tare da shugaban kasa Buhari
Shugaban Majalisar Dattawa tare da shugaban kasa Buhari
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce: "An jawo hankalin Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa zuwa wani rahoto da Sahara Reporters ta wallafa wanda ke nuna cewa Ma'aikatar Agaji da Ci gaban Al'umma, ta raba masa da sauran 'yan majalisar dokoki gurabe a aikin N-Power."

"Muna ba da shawara ga al'umma da su yi watsi da gaba daya wannan labaran karya da aka wallafa a kan Shugaban Majalisar Dattawa da sauran sanatoci."

KARANTA KUMA: Ana sa'insa tsakanin gwamnatin Oyo da iyalan Ajimobi kan wurin da za a binne gawarsa

"Ya kamata al'umma su sani cewa wannan rahotanni tatsuniyoyi ne kawai da ake yadawa domin bata sunan majalisar dattawa yayin da aka gaza bayar da tabbaci kan zargin da ake yi musu."

"Muna so mu jaddada cewa, Shugaban Majalisar Dattawa ko kuma ofishinsa ba ya da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da al'amuran daukan aikin shirin N-Power da ake gudanarwa a yanzu."

"Muna rokon kafofin yada labarai da su yi kokarin watsa rahotanni na gaskiya, ta hanyar riko da dabi'ar tabbatar da sahihanci wajen kafa hujja musamman kafin wallafa zargin da zai zama lahani ko kuma bata sunan jami'an gwamnati."

"A ƙarshe, muna sake bayar da tabbacin cewa, labarin da aka ambata yana da lahani kuma ya kamata a yi watsi da shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel