Ana sa'insa tsakanin gwamnatin Oyo da iyalan Ajimobi kan wurin da za a binne gawarsa

Ana sa'insa tsakanin gwamnatin Oyo da iyalan Ajimobi kan wurin da za a binne gawarsa

Bayanai sun bayyana a ranar Asabar cewa, wata mummunar sa'insa tsakanin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi da Gwamnatin Jihar Oyo ce ta haddasa jinkirin binne shi.

Tun a ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne, ajali ya katsewa Marigayi Ajimobi hanzari a wani Asibiti a jihar Legas bayan fama da cutar korona.

Kamar yadda addinin Musulunci ya shar'anta, ya kamata a binne tsohon gwamnan nan da nan ko kuma washegari bayan rasuwarsa sakamakon kwanan keso da ya yi.

Sai dai kawo yau Lahadi, kwanaki hudu kenan ba a binne tsohon gwamnan ba sakamakon yadda ba a cimma matsaya ba a kan wurin da za a shimfide gawarsa.

Wata majiya mai karfi da ta fito daga cikin dangin mamacin, ta bayyana cewa ana ci gaba da jinkirin binne tsohon gwamnan sakamakon cikas da gwamnatin jihar ta kawo game da shirye-shiryen gudanar da jana'izarsa.

Marigayi Abiola Ajimobi; tsohon gwamnatin Oyo
Marigayi Abiola Ajimobi; tsohon gwamnatin Oyo
Asali: Depositphotos

Majiyar ta bayyana cewa, gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin gwamna Seyi Makinde, ba ta bayar da lamuninta ba a kan binne marigayi Ajimobi duk da an tuntube ta.

Da ta ke bai wa wakilan jaridar The Punch tabbaci, majiyar ta bayyana cewa, iyalan marigayi Ajimobi sun yi shirin jana'izarsa washegari bayan rasuwarsa, amma gwamnatin jihar ta tsawatar musu.

Sai dai a yayin da aka tuntubi tsohon sakataren sadarwa a gwamnatin marigayi Ajimobi, ya musanta ikirarin da iyalan tsohon gwamnan suka yi, lamarin da ya ce uzurinsu ba ya da wata madogara bare tushe.

Mr Taiwo Adisa ya yi bayanin cewa, iyalan tsohon gwamnan sun yi shirin binne gawarsa a gidansa da ke unguwar Oluyole amma daga baya suka ce za a binne shi a Oke Ado.

Ya ce Oke Ado da iyalan mamacin sauka sauya shawarar binne shi, wuri ne da aka dade ana rigimar gado tsakanin gwamnatin jihar da marigayin.

KARANTA KUMA: Masu zanga-zanga sun lalata ofishin jakadancin Najeriya a Indonesia

A wani rahoto mai nasaba da wannan da Legit.ng ta ruwaito, wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo na binne shi a cikin masallaci.

A baya bayan ne dai kakakinsa, Bola Tunji, ya sanar da cewa a za binne shi a babban masallacinsa da ke Oke-Ado a garin Ibadan, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni da karfe 12.00 na rana.

Wannan sanarwa ta tayar da kura yayin da wasu al'ummar musulmi suka tabbatar da haramcin yunkurin bisa ga madogara ta shari'ar Musulunci.

Wakilin Legit, Ibrahim Akinola, ya tattaro cewa Musulami a fadin Najeriya sun ce abinda iyalan marigayin ke kokarin yi na binneshi cikin Masallaci Haramun ne kuma hakan zai sa mutane su daina Sallah a Masallacin.

Wani Malamin addini, Ustadh Ibrahim Tijjani, ya ce Manzon Allah (SAW) ya haramta binne Musulmai cikin Masallaci kamar yadda ya hana ginin Masallaci kan kaburbura.

Yace: "Manzon Allah (SAW) ya hana binne mutane cikin Masallaci da kuma gini kan kabari, hakazalika ya la'anci masu yin haka."

"Manzon tsira ya cewa wannan dabi'ar Yahudu da Nasara ne kuma yana iya kaiwa ga shirka."

Wani Malamin addinin, Sheik Abdullah Qasim ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce muddin aka birneshi ciki toh an kori mutane daga Masallacin domin dole a wofantar da shi.

Yace: "Al'ummar Musulmin jihar Oyo su farga, kada ku binne Sanata Ajimobi a cikin Masallacin nan. Kada ku kori mutane daga Masallacin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel