Yanzu-yanzu: Iyalan Ajimobi sun dage jana'izarsa, sun bayyana dalili

Yanzu-yanzu: Iyalan Ajimobi sun dage jana'izarsa, sun bayyana dalili

- Iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi sun dage jana'izarsa

- Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni sakamakon cutar korona da ya kamu da ita

- Bolaji Tunji, mai magana da yawun mamacin, ya ce iyalan za su kiyaye dokokin NCDC yayin jana'izar

Iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, sun sanar da dage jana'iza da birne tsohon gwamnan.

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa sun bada sanarwar ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni ta hannun mai magana da yawun marigayin, Bolaji Tunji.

Bolaji Tunji ya sanar da manema labarai sakon a garin Ibadan, cewa iyalan za su fitar da tsarin jana'izar sannan su bada sanarwa.

Legit.ng ta gano cewa Tunji ya sanar da cewa za a yi jana'izar ne ba tare da taron jama'a ba kuma cike da kiyaye dokokin hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC).

"Nan babu dadewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izarsa amma za a kiyaye dokokin hukumar kula da cututtuka masu yaduwa (NCDC)," yace.

Ya yi kira ga masu zaman makoki da ke zuwa gidan mamacin da su kiyaye dokokin NCDC ta hanyar wanke hannu, saka takunkumin fuska da yin nesa-nesa da juna.

Ajimobi ya rasu ne a wata asibiti mai zaman kanta da ke jihar Legas a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni yayin da yake da shekaru 70 a duniya.

Yanzu-yanzu: Iyalan Ajimobi sun dage jana'izarsa, sun bayyana dalili
Yanzu-yanzu: Iyalan Ajimobi sun dage jana'izarsa, sun bayyana dalili. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda Dino Melaye ya rera wakar 'ba'a' ga Oshiomhole

Kafin rasuwar Ajimobi, shine mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin kudu.

Hakazalika, an ruwaito cewa bangaren jam'iyyar APC na jihar Oyo da kuma jam'iyyar a matakin kasa baki daya na matukar bukatar fasaharsa da gogewarsa a siyasa yayin da labarin mutuwarsa ta riskesu.

An kwantar da tsohon gwamnan a asibitin First Cardiologist and Cardiovascular Consultants a ranar 2 ga watan Yuni, jinyar da bai tashi ba kenan.

Idan akwai wani abu da za a kwatanta Sanata Abiola Ajimobi da shi bai wuce basira, iya magana da kuma kwarin guiwarsa ba.

Dalilin da yasa ake masa ado da "Constituted Authority" bayan arangamarsa da dalibai masu zanga-zanga na Ladoke Akintola University (LAUTECH) a 2018.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel