Duk da matsin lambar da muke fuskanta ba za a buɗe makarantu ba a yanzu - Nwajiuba

Duk da matsin lambar da muke fuskanta ba za a buɗe makarantu ba a yanzu - Nwajiuba

A yayin ci gaba da kiraye-kirayen da ake yi wa gwamnatin tarayya a kan ta ba da umarnin buɗe makarantu, ta ce sam ba ta san zancen ba.

Gwamnatin tarayya a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana cewa, duk da matsin lamba da ta ke fuskanta, ba za ta yanke shawarar buɗe makarantu ba a yanzu.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Karamin Ministan Ilimi; Chukwuemeka Nwajiuba
Karamin Ministan Ilimi; Chukwuemeka Nwajiuba
Asali: UGC

Nwajiuba ya ce duk rintsi, ba za a yi gaggawar buɗe makarantu ba tukunna, a sakamakon fargabar da gwamnatin tarayya ta ke yi na jefa yara cikin hatsari.

Ya ce ma'aikatar ilimi ta na fuskantar matsin lamba mai tsananin gaske a kan batun buɗe makarantu, sai dai duk da hakan ba za ta sauka daga matsayarta ba tukunna.

Ministan ya ce a yanzu a manta da batun buɗe makarantu har sai an fara samun rangwamin yaduwar cutar korona a kasar nan.

“Ma’aikatar Ilimi ta na sake jadadda kudirinta na tsare lafiyar dalibai a Najeriya kuma saboda haka ba za ta yi wani abu da zai jefa lafiyarsu cikin hadari ba," inji ministan.

KARANTA KUMA: Manyan birane 5 mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika

"Gwamnatin tarayya ta na sane da ɓarnar da cutar korona ta haddasa asarar rayuka da durkusar da tattalin arziki a duniya baki daya, saboda haka ba za ta yi wani yunkuri ba yanzu wanda daga bisani zai zame mata abin da na sani."

"Ba ma son a samu ko da yaro daya da cutar korona za ta hallaka sakamakon buɗe makarantu a lokacin da bai kamata ba. Saboda haka duk wutar da za a ci gaba da huro mana a yanzu za mu jureta."

A rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, wamnatin Tarayya ta shata sharuɗa ga kafatanin makarantu da sauran cibiyoyin ilmantarwa a fadin tarayya da dole sai an cika kafin a sake buɗe su.

Sharuɗan da gwamnatin tarayya ta gindaya suna kunshe ne a cikin wata takarda mai shafi 36 wanda Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya gabatar wa Majalisar Dattawa.

Takardar wadda manema labarai na jaridar The Nation suka samu damar yin hange a kanta, an yi mata lakabi da ka'idodin sake buɗe makarantu da cibiyoyin ilimi bayan rufe su saboda annobar korona.

Mallam Adamu yayin gabatar da daftarin, ya sanar cewa wannan sharuɗa da aka shata su ne dabarun da za a aiwatar domin tabbatar da aminci da kuma ingancin sake buɗe makarantu.

Mafi muhimmancin cikin sharuɗan da aka gindaya, shi ne sai makarantu sun ƙirƙiri wuraren killace wadanda cutar korona ta harba na wucin gadi gabanin samun cancantar buɗewa.

Ya kuma zama wajibi ga duk makarantu su ƙirƙiri wata cibiyar kula da matakan dakile yaduwar cutar da za a rika kai dalibai, malamai da sauran ma'aikata yayin da suka kamu da rashin lafiya a makaranta.

Ya ci gaba da cewa, dole ne makarantu su tanadi isassun kayan aikin asibiti musamman na kare kai da kuma wuraren shan magani yadda ya dace.

Kazalika ministan ya ce za a tabbatar da kiyaye dokar sanya takunkumin rufe fuska, da kuma tanadar wadatattun wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin wanke hannu (sanitizer).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel