Manyan birane 5 mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika
- Garin Legas shi ne birni na biyu mafi tsada a nahiyar Afrika
- Birnin N'Djamena na Chadi, ya fi kowane birni tsada a nahiyar yayin da birnin Libreville na da Abidjan suka zo a mataki na uku da hudu a jere da juna
- Kasar Congo ta shiga sahun manyan birane mafi tsada, inda babban birnin kasar, Brazaville ya zo a mataki na biyar
A halin yanzu mafi tsadar birni a doron kasa shi ne birnin Hong Kong kamar yadda alkaluma suka nuna.
Kididdigar birane mafi tsadar rayuwa da aka gudanar karo na 26 a bana, ta nuna cewa birnin Hong Kong na kasar China ya ciri tuta.
Shafin Face2Face Africa ya ruwaito cewa, an gudanar da wannan bincike ne a watan Maris na shekarar 2020, yayin da ake tsaka da fama da annobar cutar korona.
An gudanar da kididdigar ne a kan manyan birane 209 cikin nahiyoyi biyar na duniya.
Legit.ng ta fahimci cewa, an yi la'akari, tsadar kudin haya, sufuri, abinci, sutura, nishadi da sauran kayayyaki na more rayuwa.

Asali: UGC
A rukunin nahiyar Afrika, birnin N'Djamena na kasar Chadi, shi ne mafi tsadar rayuwa a nahiyar, sai kuma birnin Legas na Najeriya a mataki na biyu.
Ga jerin manyan birane 5 mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika:
1. N'Djamena (Chadi)
Babban birnin Chadi shi ne na 11 cikin jerin manyan birane mafi tsadar rayuwa a duniya a kididdigar da aka gudanar a shekarar 2019. A bana ya sauka zuwa mataki na 15 a duniya.
2. Birnin Legas (Najeriya)
Birnin Legas wanda a da shi ne babban birnin Najeriya, yana daya daga cikin birane masu tarin jama'a a nahiyar Afrika. A bara ya zo a mataki na 25 cikin jerin manyan birane mafi tsadar rayuwa a doron kasa kuma na 4 a nahiyar Afrika.
A bana, birnin ya kara sama, inda ya zo a mataki na biyu cikin jerin birane mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika.
3. Libreville (Gabon)
A bana, birnin Libreville na kasar Gabon, bai gusa ko ina ba daga mataki na uku cikin birane mafi tsadar rayuwa a nahiyar Afrika kamar yadda ya kasance a bara. Shi ne birni na 33 mafi tsada a duniya a yanzu.
KARANTA KUMA: Gwamnatin Borno ta dauki matasa 2,862 aikin sharar titi da magudanan ruwa
4. Abidjan (Cote d'Ivoire)
An sanya birnin Abidjan a mataki na 4 cikin jerin manyan birane mafi tsadar rayuwa a nahyar Afrika, kuma shi ne na 36 a duniya.
5. Brazzaville (Congo)
Birni na biyar mafi tsadar rayuwa ga baki a nahiyar Afrika shi ne Brazaville, kuma shi ne a mataki na 44 a duniya.
A bara birnin Brazaville ya zo a mataki na 39 cikin jerin biranen duniya mafi tsadar rayuwa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng