Gwamnatin Borno ta dauki matasa 2,862 aikin sharar titi da magudanan ruwa

Gwamnatin Borno ta dauki matasa 2,862 aikin sharar titi da magudanan ruwa

Gwamnatin jihar Borno, ta sanar da daukan matasa kimanin 2,862 aiki shara da kuma tsaftacce magudanan ruwa a cikin Maiduguri da kewaye.

Kwamishinan ma'aikatar yaki da talauci na jihar, Nuhu Clark, shi ne ya sanar da hakan a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Maiduguri.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwato, wannan sanarwa ta Mista Nuhu ta zo ne yayin bayar da shaidar kwazon da ma'aikatarsa ta yi a cikin shekara guda da ta gabata.

Mista Clark ya sanar da cewa, matasan wanda aka dauka a karkashin shirin yaki da talauci na gwamnatin jihar, ana biyansu naira dubu 30 a kowane wata.

Gwamnan jihar Borno; Babagana Zulum
Gwamnan jihar Borno; Babagana Zulum
Asali: Twitter

Ya ce an dauki matasan aikin sharar titi da kwasar shara a cikin birnin Maiduguri da kuma tsaftace magudanan ruwa gami da yi musu feshin maganin kashe kwari musamman sauro.

Za a ci gaba da biyan matasan naira dubu 30 a kowane wata har na tsawon watanni shida, inda daga nan za a ba su tallafin jari domin su kama sana'a irin wadda suka yi ra'ayi.

KARANTA KUMA: Adadin masu cutar korona a Afirka ya zarta 330,000 - WHO

Ya kuma ce an ba wa 'yan tireda 2, 250 da ke kasuwar Kwastam da kuma ta Tashar Mairi, bashin naira dubu 30, inda ake sa ran kowanensu ya biya naira dubu 15 kacal cikin shekaru biyar.

Kwamishinan ya ce ma'aikatarsa ta kuma bayar da bashi da tsakanin na naira dubu 60 zuwa dubu 500 ga 'yan kasuwar waya ta Bulumkutu da ibtila'in gobara ya aukawa.

Ya kara da cewa, cikin watanni goma sha biyu, ma'aikatar ta aiwatar da wasu muhimman ayyuka 12 a karkashin shirin bayar da tallafi musamman ga masu rauni.

Kazalika ya ce, an bayar da tallafin kayayyakin abinci da kudi ga iyayen 'yan matan Chibok da aka yi garkuwa da su, a fafutikar da gwamnatin jihar ta ke yi na taya su damuwa da halin da suke ciki.

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hukumar gudanar ta jami’ar Bowen da ke garin Iwo a jihar Osun, ta kori ma'aikatanta sama da 100.

Shugaban sashen hulda da al'umma na jami'ar, Toba Adaramola, shi ne ya bayyana wannan rahoto cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni.

A cewarsa, jami'ar ta yanke wannan hukunci ne duba da yanayi na rayuwa da ake fuskanta a yanzu, lamarin da ya sa ba za ta iya ci gaba da rike ma'aikatan ba.

Adaramola ya ce ma'aikatan da abin ya shafa, jami'ar ta sanar da yankewar alakarta da su ta hanyar sakonnin da ta aike musu ta email, bayan biyansu albashin watan Yuni a ranar Talata.

Ya kara da cewa, kusan kashi 10 cikin 100 na ma'aikatan jami'ar sallamar aikin ta shafa da suka hadar da masu koyarwa da wadanda ba sa koyarw.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel