Adadin masu cutar korona a Afirka ya zarta 330,000 - WHO
- Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an samu mutum fiye da mutum 330,000 da suka kamu da Coronavirus a nahiyar Afirka
- Hukumar ta ce fiye da mutum 160,000 sun warke yayin da sama da mutum 8,800 suka mutu sakamakon annobar
- Rahoton da WHO ta wallafa ya nuna cewa mutum 111,796 sun kamu a Afirka ta Kudu, 22,020 a Najeriya, sai kuma 12,248 a Algeria
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, ta sanar da cewa cutar korona ta harbi sama da mutane 330,000 a nahiyar Afirka.
Reshen Hukumar WHO na Afrika da ke birnin Brazzaville a kasar Congo, shi ne ya fitar da wannan sanarwa a kan shafin dandalin sada zumunta na Twitter.
Sanarwar ta bayyana cewa, cutar korona ta harbi mutum 335,791 a nahiyar Afirka, kuma an samu mutum 160,829 da suka warke bayan kamuwa da cutar.
Haka kuma alkaluman da Hukumar ta fitar sun nuna cewa, an samu mutum 8,856 da cutar korona ta hallaka a baki daya nahiyar Afrika.

Asali: UGC
Kididdigar ta nuna cewa, kasar Afrika ta Kudu, Najeriya da kuma Algeria, sun fi sauran kasashen nahiyar yawan mutanen da cutar ta harba.
Cikin rahoton, Afirka ta Kudu tana da mutum 111,796 da suka kamu da cutar, sai kuma mutum 2,205 da cutar ta hallaka.
KARANTA KUMA: Kwayar Tramadol tana kara rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabas - NDLEA
A Najeriya cutar ta harbi mutum 22,020, sannan kuma an tabbatar da mutuwar mutum 542 a kasar.
Sai kuma kasar Aljeriya inda alkaluma suka tabbatar da kamuwar mutane 12,248, yayin da mutane 869 suka riga mu gidan gaskiya.
Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta harba cikin kowace kasa a nahiyar Afrika
Algeria – 12,248
Angola – 197
Benin – 902
Botswana – 92
Burkina Faso – 919
Burundi – 144
Cameroon – 12,592
Cape Verde – 999
Central African Republic – 3,099
Chad – 860
Comoros – 265
Congo-Brazzaville – 1,087
DR Congo – 6,213
Djibouti – 4,630
Egypt – 59,561
Equatorial Guinea – 1,664
Eritrea – 144
Eswatini – 690
Ethiopia – 5,034
Gabon – 4,956
(The) Gambia – 42
Ghana – 15,013
Guinea – 5,174
Guinea-Bissau – 1,556
Ivory Coast – 8,164
Kenya – 5,206
Lesotho – 17
Liberia – 662
Libya – 670
Madagascar – 1,787
Malawi – 941
Mali – 2,005
Mauritania – 3,519
Mauritius – 341
Morocco – 10,907
Mozambique – 762
Namibia – 76
Nijar – 1,051
Najeriya- 22,020
Rwanda – 830
Sao Tome da Principe – 710
Senegal – 6,129
Seychelles – 11
Sierra Leone – 1,354
Somalia – 2,835
Afrika ta Kudu – 111,796
Sudan ta Kudu – 1,942
Sudan – 8,889
Tanzania – 509
Togo – 583
Tunisia – 1,160
Uganda – 805
Zambia – 1,489
Zimbabwe – 530
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng