Kwayar Tramadol tana kara rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabas - NDLEA

Kwayar Tramadol tana kara rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabas - NDLEA

Muhammad Abdallah, shugaban Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ya bayyana hatsabibiyar ƙwayar da ta ke rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabas.

Ya ce ƙwayar Tramadol ita ce jigo cikin duk ababen da suke kara rura wutar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya ki ci ya ki cinyewa.

Ya tabbatar da cewa, yadda mutane ke shan miyagun kwayoyi ya karu sakamakon zaman gidan da ake ci gaba da yi sanadiyar dokar kulle da aka shimfida saboda annobar korona.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, shugaban na NDLEA ya ce a yanzu shan miyagun kwayoyi ita ce ainihin annobar da ake fuskanta a kasar nan.

Furucin hakan ya zo ne a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai dangane da shirin bikin zagayowar ranar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi da safarar bil Adama ta Duniya ta bana.

Legit.ng ta fahimci cewa, za a gudanar da bikin ranar yaki da muggan kwayoyi ta wannan shekara a ranar Juma'a, 26 ga watan Yuni.

Ma'aikatan NDLEA a bakin aiki
Ma'aikatan NDLEA a bakin aiki
Asali: UGC

Mista Abdallah ya bayyana damuwarsa kwarai dangane da yadda shan ƙwayar Tramadol ta yi ƙamari a tsakanin matasan Najeriya.

Shugaban Hukumar NDLEA ya ce "a yanzu gwamnatin kasar Indiya ta sanya idanun lura tare da takaita yadda ake shigo da ƙwayar Tramadol zuwa Najeriya."

Ya ce "ana amfani da nauyin miligiram tsakanin 50 zuwa 100 na ƙwayar Tramadol a matsayin magani, amma abin mamaki shi ne yadda matasa ke shan ta babu ka'ida."

Ya ke cewa, "a lokaci daya wasu matasa su kan sha miligiram 200 ko 500 na ƙwayar Tramadol, wanda ko ƙwaƙwalwar doki ba za ta iya dauka ba a lokaci guda."

"Amma wannan ita ce ƙwayar da 'yan Najeriya ke sha. Irin wannan abu shi ke kara rura wutar ta'addanci a Arewa maso Gabas."

"Domin kuwa Kwamandu daban-daban na rundunar soji sun tabbatar da shaidar hakan da cewa a duk sansanin 'yan Boko Haram da suka kai simame sai sun samu miyagun ƙwayoyin musamman Tramadol."

KARANTA KUMA: Duk da musibar Boko Haram, UNIMAID ta fi kowace jami'a a Najeriya daukan dalibai a shekarar 2019

Yayin ci gaba da babatu, Mista Abdalla ya ce a kowace kasa ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ba ya haura kashi 5%, amma abun takaici a Najeriya lamarin ya doshi kashi 15%.

"Wannan kididdiga ta alkaluma ba abu ne da za mu yi farin cikin da ita ba."

Kazalika ya bayyana damuwa dangane da yadda hukumar NDLEA ta ke fama da karancin ma'aikata da za su yaki ta'ammali da fataucin miyagun ƙwayoyi a kasar nan.

Ya nemi iyaye da su taimaka wajen sanya ido a kan 'ya'yansu, lamarin da ya ce wannan yaki ne na mu duka.

Ya kara da cewa, gwamnati ta fara shirin daukar mataki na shawo kan matsalar karancin ma'aikata da Hukumar ta ke fuskanta, inda ya ce shugaban kasa ya ba da umarnin daukar karin ma'aikata.

"Ba sai an fada ba, ma'aikata 5,000 ba za su iya yakar ta'ammali da fataucin miyagun ƙwayoyi ba a kasar nan yadda ya dace."

"Bari na lissafa kananan hukumomi uku kacal na kasar nan da duk ma'aikatan hukumar NDLEA har ni kai na ba za su wadatar ba; kun san Mushin a jihar Legas, kun san Fagge a jihar Kano ko kuma Nyanya a Abuja."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel