Jami'ar Bowen ta sallami ma'aikata sama da 100

Jami'ar Bowen ta sallami ma'aikata sama da 100

Hukumar kula da jami’ar Bowen da ke garin Iwo a jihar Osun, ta kori ma'aikatanta sama da 100 kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Shugaban sashen hulda da al'umma na jami'ar, Toba Adaramola, shi ne ya bayyana wannan rahoto cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni.

A cewarsa, jami'ar ta yanke wannan hukunci ne duba da yanayi na rayuwa da ake fuskanta a yanzu, lamarin da ya sa ba za ta iya ci gaba da rike ma'aikatan ba.

Adaramola ya ce ma'aikatan da abin ya shafa, jami'ar ta sanar da yankewar alakarta da su ta hanyar sakonnin da ta aike musu ta email, bayan biyansu albashin watan Yuni a ranar Talata.

Ya kara da cewa, kusan kashi 10 cikin 100 na ma'aikatan jami'ar sallamar aikin ta shafa da suka hadar da masu koyarwa da wadanda ba sa koyarwa.

Jami'ar Bowen
Hakkin mallakar hoto: Jaridar Premium Times
Jami'ar Bowen Hakkin mallakar hoto: Jaridar Premium Times
Asali: UGC

Cikin sanarwar da Adaramola ya fitar, ya ce "hukumar gudanar da jami'ar ta yanzu wadda ta karbi ragamar aiki a shekarar 2018, ta gano cewa akwai bukatar a sake sauya fasalin jami'ar."

"Bayan dogon nazari da bincike da aka gudanar, an gano cewa dole ne a sauya al'adu da tsare-tsaren gudanar da jami'ar domin ta iya ci gaba da tsayawa da kafarta."

"Domin jami'ar ta ci gaba da wanzuwa da kasancewa, dole ne tayi tankade da rairayen wasu daga cikin ma'aikatanta tare da yin duba izuwa ga cancanta."

KARANTA KUMA: Duk da musibar Boko Haram, UNIMAID ta fi kowace jami'a a Najeriya daukan dalibai a shekarar 2019

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya zo ne makonni bayan da Jami'ar Amurka ta Najeriya (AUN) da ke birnin Yola a jihar Adamawa, ta sallami kusan ma'aikatanta 400.

A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, Jami'ar AUN mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ta kori ma'aikata fiye da 400.

Korar ma'aikatan na zuwa ne a cikin kwanaki uku kacal bayan wani kamfanin sadarwa na Atiku mai suna 'Gotel Communications' ya kori ma'aikata 46.

A takardar korar ma'aikatan, mai dauke da sa hannun shugaban AUN, Dawn Dekle, jami'ar ta ce ba ta da bukatar aiyukan ma'aikatan da ta kora, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

Wasu daga cikin ma'aikatan da aka kora sun shaidawa SaharaReporters cewa an koresu ba tare da biyansu kowanne alawus ba duk da cewa sun shafe fiye da shekara 10 su na aiki a jami'ar.

Sai dai, Abubakar Abba Tahir, mataimakin shugaban jami'ar mai kula da hulda da jama'a, ya musanta zargin ma'aikatan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng