Duk da musibar Boko Haram, UNIMAID ta fi kowace jami'a a Najeriya daukan dalibai a shekarar 2019

Duk da musibar Boko Haram, UNIMAID ta fi kowace jami'a a Najeriya daukan dalibai a shekarar 2019

Alkaluman da hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i a Najeriya (JAMB) ta fitar, sun nuna cewa jami'ar Maiduguri, UNIMAID, ta fi kowacce jami'a daukan dalibai a bara.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, jami'ar UNIMAID ta yi wa sauran jami'o'in kasar zarra a bara duk da yadda ake fama da musibar ta'addancin kungiyar Boko Haram.

A bara jami'ar ta bai wa dalibai 12,523 gurbin karatu, doriya a kan dalibai 11,665 da ta bai wa a shekarar 2018.

Jami'ar tana nan a wajen birnin Maiduguri daura da hanyar garin Bama, inda ya kasance cibiyar da ta'addancin Boko Haram ya tsananta tsawon shekaru.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'ar ba ta kubuta daga hare-haren Boko Haram ba, yayin da kungiyar ta lashi takobin nuna kiyayya da ilimin Boko.

Kungiyar ta kashe dubun dubatan mutane tare da mayar da miliyoyin mutane 'yan gudun hijira a Arewacin Najeriya.

A shekarar 2017, wani hari na tagwayen bama-bamai da aka kai jami’ar, kashe mutane hudu, ciki har da wani malami, Farfesa Aliyu Mani, da kuma daya daga cikin maharan.

KARANTA KUMA: Faiq Bolkiah: Tauraron Leicester City ya bayyana a matsayin ɗan kwallo mafi arziki a duniya

Sai dai a yayin da manema labarai suka tuntuba, jami'in hulda da al'umma na jami'ar, Ahmed Muhammed, ya ce an samu karin yawan dalibai dake son yin karatu a jami’ar ne saboda tsaro da aka sa.

Ya na mai cewa, "baya ga tsaro da aka saka na jami’an sojoji, ita kanta jami’ar ta kafa nata jami’an tsaron na ‘yan banga da mafarauta domin samar da tsaro a makarantar."

"Sannan kuma idan baka da shaidar ko kai wanene ba za a barka ka shiga jami’ar ba."

Ga jerin Jami'o'i 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019

Cikin kowane dalibi shida da aka dauka a makarantun gaba da sakandire a bara, akalla daya daga cikinsu ya samu gurbin karatu ne a jami'o'in nan goma kamar yadda alkaluman hukumar JAMB suka nuna.

Jerin jami'o'i 10 da suka fi bayar da gurbin karatu a 2019
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Jerin jami'o'i 10 da suka fi bayar da gurbin karatu a 2019 Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Asali: UGC

Wannan jami'o'i 10 sun dauke kashi daya bisa shidan guraban karatu da aka bayar a bara. Ga sunayensu da adadin guraban karatu da suka bayar a 2019.

 1. Jami'ar Maiduguri - 12,435
 2. Jami'ar Calabar - 12,237
 3. Jami'ar Benin - 11,747
 4. Jami'ar Ilori - 11,616
 5. Jami'ar Legas - 9,625
 6. Jami'ar Fatakwal - 9,107
 7. Jami'ar Nnamdi Azikwe - 8,880
 8. Jami'ar Najeriya, Nsuka - 8,585
 9. Jami'ar Jihar Ekiti, EKSU - 8,119
 10. Jami'ar Jihar Ribas, RSU - 7,843.

Ga jerin Kwalejojin Kimiyya da Fasaha 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019

Jerin Kwalejojin Kimiyya da Fasaha 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Jerin Kwalejojin Kimiyya da Fasaha 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019 Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Asali: UGC
 1. Kaduna Polytechnic, Kaduna - 7,897
 2. Yaba College of Technology, Yaba, Lagos - 4,046
 3. The Polytechnic, Ibadan, Oyo - 3,270
 4. Akanu Ibiam Federal Polytechnic, Unwana, Ebonyi - 3,212
 5. Plateau State Polytechnic, Barkin-Ladi - 3,024
 6. Lagos State Poly, Ikorodu - 2,822
 7. Federal Polytechnic, Offa, Kwara - 2,711
 8. Federal Polytechnic, Ilaro - 2,646
 9. Ogun State Institute of Tech (wadda a da ake kira Gateway ICT Poly), Igbesa - 2,471
 10. Federal Polytechnic, Ado-Ekiti - 2,432

Ga jerin Kwalejojin koyan aikin malunta 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019

Jerin Kwalejojin koyan aikin malunta 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019
Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Jerin Kwalejojin koyan aikin malunta 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019 Hakkin Mallakar Hoto: Jaridar Premium Times
Asali: UGC
 1. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, F.C.E Pankshin, Plateau - 4,828
 2. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, F.C.E Kano - 4,793
 3. Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya, F.C.E Gombe - 4,720
 4. Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna, Gidan-Waya - 4,276
 5. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, F.C.E Zaria - 4,188
 6. Kwalejin Ilimi ta Akwanga, Nasarawa - 2,923
 7. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, F.C.E Oyo - 2,771
 8. Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Dutsin-Ma, Katsina - 2,735
 9. Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya, F.C.E, Potiskum, Yobe - 2,650
 10. Kwalejin Ilimi ta Tarayya, F.C.E Osiele, Abeokuta - 2,638

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel