Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 649 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 649 sun kamu da cutar korona a Najeriya

Alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa na ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, ya bayyana cewa mutum 649 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya.

A jihar Legas an samu sabbin masu cutar 250, jihar Oyo an samu karin mutum 100 sai jihar Filato an samu karin mutum 40 da ke dauke da cutar.

A jihar Delta an samu karin mutum 40 sai jihar Abia inda aka samu karin mutum 28 yayin da aka samu karin mutum 27 a jihar Kaduna.

A jihar Ogun an samu karin mutum 22, jihar Edo an samu karin mutum 20, sai kuma jihar Akwa Ibom inda aka samu karin mutum 18.

A jihar Kwara an samu karin mutum 17, babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja an samu sabbin masu cutar har 17 yayin da jihar Enugu ta samu karin mutum 14.

A jihohin Neja da Adamawa an samu karin mutum goma sha uku-uku, sai jihar Bayelsa an samu sabbin mutum 7 da ke dauke da cutar.

Jihohin Osun da Bauchi sun samu karin mutum shida-shida sai jihar Anambra da ke da karin mutum hudu.

A jihar Gombe akwai karin mutum 3, yayin da jihar Sokoto ta samu karin mutum biyu. Jihohin Imo da Kano sun samu karin mutum daddaya.

Jimillar masu cutar a Najeriya ta kai 22,020 yayin da mutum 7613 aka sallamesu daga asibiti. Mutum 542 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel