Operation Hadarin Daji: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan daban daji a Katsina da Zamfara

Operation Hadarin Daji: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin 'yan daban daji a Katsina da Zamfara

A yunkurin da ta ke yi na kakkabe masu tayar da zaune tsaye a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, rundunar sojin saman Najeriya ta kaddamar da wani sabon aiki mai suna Operation Wutar Daji.

Wannan sabon aikin hadin gwiwa da rundunar sojin ta kaddamar wani bangare na Operation Sharar Daji da ta saba gudanarwa a yankunan biyu na Arewacin Kasar.

Rahoton hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami'in sadarwa da hulda da al'umma na rundunar dakarun tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce makusudin wannan aikin hadin gwiwa da dakarun ke gudanarwa ta sama da kasa, shi ne kawo karshen 'yan daban daji da suka addabi jihar Katsina da wasu sassa a jihar Zamfara.

Manjo Janar Enenche ya ce rundunar tana ci gaba da samun nasarar kai hare-hare a sansanonin 'yan fashi da makami biyo bayan samun wasu bayanan sirri gami da leken asiri.

Shugaban hafsan sojin saman Najeriya; Air Marshal Sadique Abubakar
Shugaban hafsan sojin saman Najeriya; Air Marshal Sadique Abubakar
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, tun da aka kaddamar da aikin a ranar 20 ga watan Yuni, rundunar sojin ta kai hari wurare goma da hakan ya yi sandiyar 'yan fashi da makami sun kwanta dama.

Wasu daga hare-haren da aka samu gagarumar nasara sun hadar da na yankin Dutsen Asolo da Birnin Kogo a jihar Katsina, sannan kuma sansanin Dogo Gide a Dajin Kuyanbana da ke jihar Zamfara.

Harin da aka kai Dutsen Asolo da jiragen sama, an tarwatsa maboyar 'yan ta'adda inda da dama sun rasa rayukansu.

KARANTA KUMA: Sojoji sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Wasu daga cikin masu tayar da kayan bayan da suka tsira daga harin na farko, an sake yi musu tara-tare a wani kogon dutse, inda a nan ruwa ya karewa dan kada.

A ranar 21 ga watan Yuni kuma, an yi amfani da wani jirgin yaki mai saukar ungulu, wajen yi wa sansanin 'yan ta'adda da ke Dajin Kuyanbana ruwan wuta.

Haka zalika a ranar 22 ga watan Yuni, wasu 'yan ta'adda da suka tsere daga sansaninsu zuwa dokar daji bayan jin sautin barin wuta da jiragen dakaru ke yi, su ma sun yi gudun gara sun fada gidan zago.

Shugaban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, wanda ya kasance a jihar Katsina domin sa ido kan aikin dakaru na Operation Hadarin Daji, ya yaba da kwarewarsu.

Yayin da ya ke neman dakarun a kan kada su yi kasa a gwiwa, ya ce kada su yi wa 'yan ta'adda rangwami har sai sun ga bayansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel