Gwamnatin Tarayya za ta yanke shawara kan dokar hana zirga-zirga a mako mai zuwa - PTF

Gwamnatin Tarayya za ta yanke shawara kan dokar hana zirga-zirga a mako mai zuwa - PTF

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya, PTF, ya bayyana cewa ya fara nazari kan tsare-tsaren da za a shimfida domin cire dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.

A yayin zaman karin haske kan lamarin cutar korona da aka saba gudanarwa a kowace rana, kwamitin ya ce ya fara duba ka'idodin yadda za a dawo da zirga-zirga tsakanin jihohi.

Da ya ke magana a ranar Litinin cikin birnin Abuja, babban jami'i a kwamitin, Dr. Sani Aliyu, ya ce za a bude tituna da zarar tashoshin mota a fadin tarayya sun tanadi matakan hana kamuwa da cutar korona.

Furuncin Dr. Aliyu ya zo ne a yayin da shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya ba da sanarwar cewa, gwamnatin tarayya za ta yanke hukunci a mako mai zuwa game da dokar kulle ciki har da dokar haramcin zirga-zirga tsakanin jihohi.

Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya, PTF
Kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya, PTF
Asali: Twitter

Babban jami'i a kwamitin, ya ce a halin yanzu ana nazari kan ka'idodin da karamar ministar sufuri, Gbemisola Saraki ta gabatar, kuma za a bude hanyoyin da zarar an tabbatar da amincin aiwatar da hakan.

Ya ce: "har yanzu haramcin hana zirga-zirga a tsakanin jihohi yana nan, amma muna tattaunawa da ma'aikatar sufuri domin cimma matsayar da za ta bai wa al'umma damar ci gaba da sararawa."

"Daga cikin sharudan da ma'aikatar sufuri ta shata shi ne tabbatar da an tanadi wuraren wanke hannu karkashin ruwa mai gudana a duk tashoshi da garejin motoci."

"Sai tabbatar da an kiyaye dokar nesa-nesa da juna da kuma bayar da tazara ta hanyar rage yawan fasinjojin da za a rika dauka a kowace mota daya."

KARANTA KUMA: 'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar

"Kuma ina kyautata zaton ma'aikatan motocin haya sun fara aiki kan wannan batu, kuma da zarar mun samu aminci a kan hakan, za a bude tituna domin al'umma su ci gaba da walwala."

Dr Aliyu wanda ya nuna damuwarsa game da rashin bin ka'idodin kariya da na dakile yaduwar cutar korona, ya roki gwamnatocin jihohi da su kara kaimi wajen yiwa al'umma gwajin cutar.

Haka zalika, ya nemi gwamnatocin jihohi da su tilastawa al'ummarsu sanya takunkumin rufe fuska yayin shiga taron jama'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel