'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar

'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar

A yayin da lamarin tsaro ya ke ci gaba da tabarbarewa a kasar, Sufeto Janar na 'Yan sanda, Muhammadu Adamu, ya ce kada a yi tunanin 'yan sanda za su iya kasancewa ko ina a koda yaushe.

A ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, babban jami'in dan sandan ya ce 'yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe domin bai wa al'umma kariya.

Sufeton na 'yan sanda ya yi furucin hakan ne yayin bikin kaddamar da kwamitin ba da shawara kan harkar tsaro, wanda Sarkin Gombe, Shehu Abubakar da kwamishinan 'yan sandan jihar, Maikudi Shehu suka jagoranta.

Adamu wanda mataimakin sufeto janar na 'yan sanda, Halliru Gwandu ya wakilta, ya ce babu wani lokaci mafi dace da ya kamata a kaddamar da wannan kwamiti face yanzu.

Sufeto Janar na 'yan sanda; Muhammad Adamu
Sufeto Janar na 'yan sanda; Muhammad Adamu
Asali: Twitter

A nasa jawaban, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce tsaro na da matukar muhimmanci kuma matukar ba a tsaya tsayin-daka wajen inganta shi ba, zaman lafiya ba zai wadata ba.

"Abu mafi fifiko ga kowacce gwamnatin shi ne samar da tsaro, saboda idan aka samu tsaro, za a iya bayar da tabbacin cewa za a kare rayuka kuma za a ci gaba da harkokin kasuwanci," in ji Yahaya.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne gwamnonin jihohi 19 na Arewa suka gana da shugabannin tsaro na kasa a ofishin mai ba da shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno.

KARANTA KUMA: Ya kamata Najeriya ta dauki mataki kan harin da aka kai mata a kasar Ghana - Gbajabiamila

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara shi ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar sirri tare da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

A makon jiya ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaro na kasa da su gana da gwamnnonin Arewa domin bijiro da matakan kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Gwamna Matawalle yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, ya ce gwamnatinsa tuni ta fara shimfida dabarun magance sha'anin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a jiharsa.

Ya yi bayanin cewa, 'yan ta'addan da suka tuba kuma suka rungumi zaman lafiya an maido su cikin al'umma, yayin da wadanda suka juya baya a kan hakan za su fuskanci fushin hukuma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel