Ya kamata Najeriya ta dauki mataki kan harin da aka kai mata a kasar Ghana - Gbajabiamila

Ya kamata Najeriya ta dauki mataki kan harin da aka kai mata a kasar Ghana - Gbajabiamila

Majalisar Wakilai ta ce dole ne Najeriya ta dauki mataki kan harin da aka kai wa ofishin jakadancinta a kasar Ghana, domin irin wannan lamari ya fara wuce gona da iri.

Da yake magana cikin birnin Abuja a ranar Talata, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilan, ya ce nuna dattako na diflomasiya ta hanyar neman afuwa ba zai magance matsalar ba.

Ana iya tuna cewa, an ranar Asabar ne wasu mutanen suka rusa wasu gidajen kwana na ma'aikata a farfajiyar ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra, babban birnin kasar Ghana.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, mutanen da ba a san ko su waye ba sun kai hari na kan gidajen da ko kammala gininsu ba a yi ba.

Wannan lamari ya janyo ɓacin rai da kuma sake tayar da batun rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Daga bisani wani Sarkin gargajiya a Ghana ya yi ikirarin cewa, wurin da ake ginin gidajen filaye ne mallakar masarautarsa da aka kwace daga hannunta da karfin tsiya.

Kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila
Kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila
Asali: Twitter

Yayin da ministan harkokin waje, Geoffery Onyeama ya bayyana a gaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar a ranar Talata, kakakinta ya bayyana ɓacin ransa matuka a kan lamarin.

Gbajabiamila ya ce "wasu kasashen Afrika suna kai mana hari amma sai mu rika kawar da ido da don kada zumuncin da ke tsakaninmu da su ya lalace."

Ya ce "ramuwa ta halatta a tsarin dangantaka da kasashen ketare, kuma za mu iya amfani da wannan tsari."

"Domin kuwa da a ce a nan Najeriya lamarin ya faru, da tuni sun garzaya kotu domin ta bi musu haƙƙinsu."

"Ina so ku sani cewa tsarin dimokuraɗiyya ake yi a ƙasar Ghana inda ake amfani da doka, amma wadanda suka kai harin sun dauki hukunci ne a hannunsu.

"Saboda haka harin da aka kai wa Najeriya da gayya aka kai shi domin kuwa ba kuskure bane."

“Hakika game da batun mallakar kadarori, abu ne mai kyau mu fahimci cewa dukkan kasashe suna wanzuwa ne ta hanyar ofishin jakadancinsu a wasu kasashen.

"Wannan abu da ya faru ya ragewa Najeriya daraja a matsayinta na kasa saboda ba takaddama ba ce ta filaye tsakanin Najeriya da kowane mutum ba, amma takaddama ce ta diflomasiya tsakanin Najeriya da Ghana."

"Kuma ya kamata a bi tsarin diflomasiya ta hanyar da ta dace, saboda wadanda suka aikata hakan sun yi ne a karkashin damar da dokar kasarsu ta basu."

KARANTA KUMA: Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 20, 000 - NCDC

"Kasar Afrika ta Kudu ta yi, amma mun yi shiru, Ghana ta yi kuma muna kokarin kawar da kai don kawai mu nuna dattako da diflomasiya ta hanyar bukatar a nemi gafarar mu kuma mu dauki asara."

"Idan da a ce hakan a kan ofishin jakadancin Birtaniya da ke Ghana ta kasance, da tuni labari ya sha ban-ban."

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya kira takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari kan lamarin da ya faru.

Yayin hirarsu ta wayar tarho a ranar Talata, Akufo-Addo ya bayyana nadamarsa tare da neman afuwa a kan abinda ya faru har ya fusata gwamnati da 'yan Najeriya.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a daren ranar Talata.

Akufo-Addo ya bawa shugaba Buhari tabbacin cewa ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin tare da bashi tabbacin cewa za a hukunta masu hannu a rushe ginin.

A wata majiyar, an bayyana cewa an kama wadanda ake zargin suna da hannu a rushe ginin kuma za a gurfanar dasu a gaban kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel