Yadda mai buga iskar taya ya sace dan kamfan kwastoma

Yadda mai buga iskar taya ya sace dan kamfan kwastoma

Wani mai aikin buga iska a taya mai suna Dele Ope mai shekaru 22 ya shiga hannun jam'ian tsaro bayan ya sace dan kamfai na kwastomarsa a gidanta da ke jihar Ogun.

A wata takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun , Abimbola Oyeyemi ya fitar, ya ce budurwar ta kira Ope don ya gyara mata tayar motarta da tayi faci.

Amma kuma bayan ya kammala gyaran tayar ya tafi, sai ta nemi 'yan kamfan da ta shanya a igiya ta rasa.

An fara neman mai buga iskar tayar motar da gaggawa saboda shi kadai ne ya ziyarci gidan a wannan lokacin.

"Tunda mai buga iskar ne mutum daya da ya ziyarci gidan, ta bazama nemansa amma bata ganshi ba," kakakin rundunar 'yan sandan ya ce.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce budurwar ta kai rahoton abinda ya faru a ofishin 'yan sanda da ke Warewa.

DPO din ofishin, SP Folake Afeniforo ta yi bayani ga wasu jami'an tsaron inda suka bazama neman mai buga iskar.

Bayan binciken gidansa da aka yi, an samo dan kamfan budurwar.

Yadda mai buga iskar taya ya sace dan kamfan kwastoma
Yadda mai buga iskar taya ya sace dan kamfan kwastoma. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hadimin gwamna ya kona makwabtansa da ya yi mugun mafarki da su (Hotuna)

"Bayan bincikarsa da aka yi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya sata ne da niyyar ya kai wa bokan da zai mishi sihirin kudancewa," Oyeyemi yace.

Kwamishina 'yan sandan jihar Ogun ya bada uamrnin mika wanda ake zargin gaban kotu bayan an kammala bincikarsa.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda babban birnin tarayya da ke Abuja ta damke wasu mutum 24 da ake zargin su da laifukan da suka hada da amfani da sakon banki na bogi wurin biyan kayan da suka siya tare da biyan karuwan da suka yi lalata da su.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Frank Mba, ya ja hankalin mutane da su gane cewa ana amfani da sakon banki na bogi wurin siyan kaya da damfarar mutane.

Kamar yadda yace, an kama kashi na farko na masu laifin wadanda suka kware a tura sakon bogi na kudi daga banki ga wadanda suka damfara.

Ya ce an kama su ne bayan sun biya wasu karuwai da wannan sakon bogin. Amma kuma, ya yi kira ga jama'a da su kiyaye da yadda jama'a ke zuwa siyan kaya sannan su ce za su biya ta yanar gizo.

Shugaban kungiyar 'yan ta'addan wanda ya zanta da manema labarai a kan ayyukan kungiyar, ya tabbatar da cewa wannan sakon bankin na daukan mintuna kalilan ne kafin ya bace daga waya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel