Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF za ta yi taro a ranar Laraba

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF za ta yi taro a ranar Laraba

A gobe Laraba, 24 ga watan Yuni, ana sa ran gwamnonin tarayyar kasar nan za su gana a tsakaninsu dangane da wasu muhimman lamura da suka shafi kasar.

Gwamnonin jihohi 36 karkashin kungiyarsu ta Nigeria Governors' Forum, NGF, za su gana daga nesa ta hanyar bidiyo domin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar korona.

An ruwaito cewa, gwamnonin za su yi bita da nazari kan sake kudaden da za a batar wajen gine-gine a wasu jihohi biyar da suka hadar da; Rivers, Bayelsa, Cross River, Ondo da kuma Osun.

Sanarwa da Darekta Janar na kungiyar NGF, Mista Asishana Bayo Okauru ya fitar, ya ce gwamnonin za kuma su tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kiwon lafiya, tattalin arziki da sauransu.

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF
Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF
Asali: Twitter

Haka kuma wata sanarwa da jami'in hulda da al'umma na NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar, ya ce gwamnonin za su yi bita kan fushin da kungiyar likitoci NARD ta yi da har ya sanya ta shiga yajin aiki a makon jiya.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, Ministan ilimi, Dr. Osagie Ehanire, zai yi wa gwamnonin karin haske kan dabaru da tsare-tsaren da za a bijiro da su domin tunkarar annobar korona.

Kungiyar gwamnonin za kuma ta yi bita kan karin haske da gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, zai yi a kan sakamakon binciken da kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona ya gabatar.

A bangaren tattalin arziki, gwamnonin za su yi nazari a kan raguwar samun kasafin kudin jihohinsu daga asusun gwamnatin tarayya na FAAC.

KARANTA KUMA: Kungiyar kwadago ta dakatar da shiga yajin aiki kan ragewa ma'aikatan Kano albashi

Za kuma su tattauna kan batun sabon tsarin sauke nauyin bashin gwamnatin tarayya da ya rataya a wuyansu.

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, za kuma a kawo ajandar majalisar tattalin arziki ta kasa NEC wanda kwamitin da gwamna Nasir El-Rufa'i yake jagoranta zai warware kudirin da ta gabatar.

A karshe, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, zai gabatar da jawabai a yayin ganawa ta wayar tarho da wakilin Bankin Duniya, Yue Man Lee, kan batun sabbin tsare-tsaren shige-da-ficen kudi da za a kawo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel