Babu wata jiha a Najeriya da ta tsarkaka daga cutar korona - NCDC

Babu wata jiha a Najeriya da ta tsarkaka daga cutar korona - NCDC

- Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC), ta ce babu jihar da babu cutar korona a fadin tarayyar kasar

- Ta ce duk jihar da babu ma a yanzu, to sannu a hankali za ta samu

- NCDC ta yaba da yadda wasu jihohi hudu a kasar dangane da kwazon da suke na yaki da cutar

A yayin da adadin masu cutar korona ke ci gaba da karuwa a kasar, Dr Chikwe Ihekweazu, shugaban Cibiyar NCDC, ya bayyana cewa babu jihar da ta tsarkaka daga cutar a Najeriya.

Yayin zaman karin haske da aka saba gudanarwa a kowace rana dangane da lamarin cutar korona, Dr. Chikwe ya ce babu wata jiha a kasar nan da ta ke da garkuwar hana bullar cutar a cikinta.

Shugaban na NCDC ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai bayan zaman kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona da aka gudanar a birnin Abuja.

Dr. Chikwe ya ce duk jihar da babu cutar a fadin Najeriya to sannu a hankali za ta bulla a cikinta.

Yayin ci gaba da yi wa manema labarai bayani, Dr. Chikwe ya yabawa kwazon wasu jihohi a kasar da suke ba da himmar gaske wajen yakar wannan annoba.

Shugaban NCDC; Dr Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Dr Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Jihohin kamar yadda Dr. Chikwe ya bayyana sun hadar da Akwa Ibom, Filato, Edo, da kuma Legas.

Sai dai ya bayyana damuwa dangane da yadda wasu 'yan Najeriya ke bijerewa dokokin da mahukuntan lafiya suka shar'anta na hana kamuwa da cutar.

KARANTA KUMA: Shirin gwamnatin Oyo na bude makarantu ba daidai bane - Gwamnatin Tarayya

A halin yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya.

Kamar yadda alkalumman NCDC suka nuna cewa a ranar Litinin an gano karin mutum 675 da suka kamu da cutar korona a Najeriya, yanzu jimillar mutanen da cutar ta harba ya kai 20, 919.

Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel