Hadimin gwamna ya kona makwabtansa da ya yi mugun mafarki da su (Hotuna)
Thomas Obi Tawo wanda aka fi sani da Janar Iron, an zargesa da kona wasu mazauna yankin sa da garwashi saboda ya gansu a mafarki suna dambe kuma har sun cutar da shi.
Obi Tawo mai bada shawara na musamman ne ga gwamnan Ben Ayade na jihar Cross Rivers a kan tsaron daji.
Kamar yadda dan jarida Agba Jalingo ya bayyana, Tawo ya azabtar da mazauna yankin ta hanyar kona musu sassan jikinsu da wuta tare da tirsasasu yi masa bayani game da mafarkinsu da yayi.
Jalingo ya rubuta "Ga abinda mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ayade ya aikata. Thomas Obi Tawo wanda aka fi sani da General Iron a karamar hukumar Boki ta jihar Cross River ya yi mafarkin cewa yayi fada da wasu mutane.
"Daga nan yaje har gidajensu ya dauke su inda ya dinga kona su da wuta don su bayyana mishi gaskiyar lamarin."

Asali: Twitter
KU KARANTA: Yadda matar aure ta yi wa tsohuwar budurwar mijinta tsirara tare da tura mata kwalba a gaba

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng