Da duminsa: Mutum 675 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 20,919

Da duminsa: Mutum 675 sun sake kamuwa da korona, jimilla ta kai 20,919

A yau ranar Litinin, 22 ga watan Yunin 2020, alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC), sun nuna cewa mutum 675 suka sake kamuwa da cutar korona a Najeriya.

A jihar Legas an samu sabbin masu cutar 288, jihar Oyo ta samu sabbin masu cutar 76 sai kuma jihar Ribas da take da sabbin masu cutar 56.

A jihar Delta an samu sabbin masu cutar korona 31, Ebonyi an samu mutum 30 sai jihar Gombe da ta samu karin mutum 28.

A jihohin Ondo, Kaduna da Kwara, an samu karin mutum ashirin-ashirin. Jihar Ogun ta samu karin mutum 17 sai kuma babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta samu karin mutum 16.

Jihar Edo ta samu karin mutum 13, jihar Abia ta samu karin mutum goma yayin da jihohin Nasarawa da Imo suka samu karin mutum tara-tara.

A jihohin Bayelsa, Borno da Katsina, an samu sabbin masu cutar takwas-takwas. Jihohin Sokoto da Bauchi sun samu sabbin masu cutar uku-uku yayin da jihar Filato ta samu karin mutum biyu.

A halin yanzu, jimillar masu cutar a Najeriya sun kai 20,919 yayin da aka sallami mutum 7,109 daga asibiti bayan warkewarsu.

Mutum 525 sun rasa rayukansu sakamakon muguwar annobar da ta game duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel