Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)

Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya yi kira ga manyan hafsoshin soji da kwamandojinsa da su tashi tsaye don kawo karshen annobar rashin tsaro da ta addabi kasar nan.

Mukaddashin daraktan hulda da jama'a, Sagir Musa, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a kan abinda suka tattauna da Buratai tare da manyan hafsin sojin a ranar Litinin a Abuja.

Buratai ya ce taron an yi shi ne don janyo hankalin rundunar don yakar 'yan ta'addan Boko Haram da kuma 'yan bindiga da suka addabin yankin arewa maso yamma.

Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)
Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Ya ce sun tattauna al'amuran tsaro yayin taron tare da kuma bukatar kwamandojin, hafsin sojin da kananan sojojin da su ninka kokarinsu tare da tabbatar da cewa duk wani kalubalen tsaro ya zama tarihi.

Janar Buratai ya umarci dukkan sojojin da su tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shawo kan kalubalen tsaro.

"'Yan ta'addan da dukkan wadanda suke hada kai da masu daukar nauyinsu dole a fallasa su, bankadosu tare da tarwatsa su.

"Tuni rundunar sojin Najeriya ta aiwatar da sabbin tsari na ayyuka kuma dole ne kwamandoji su fita filin daga don ganin yadda rundunar da ke karkashinsu ke aiki."

Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)
Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kambari: Kabila a Najeriya da har yau suke yawo tsirara (Hotuna)

Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)
Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Shugaban rundunar sojin ya ja hankalin dakarun a kan cewa babu abinda yake bukatar gani da ya wuce sauyi nagari tare da sauyin da zai shafi tsaron kasar nan.

Ya tabbatar musu da cewa, a halin yanzu babu lokacin korafi ko bada wani uziri. Ya kara da cewa ba zai lamunci wani nakasu ko rashin nasara ba a wurin kokarin gyara yanayin tsaron kasar nan.

Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)
Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa rundunar sojin za ta ci gaba da hada kai da sauran cibiyoyin tsaro don kawar da dukkan nau'in rashin tsaro a kasar nan.

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yi kira ga hafsoshin tsaro da su zage damtse domin gudun saukesu daga mukamansu.

A yayin zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, Lawan ya jajanta yadda rashin tsaro ya tsananta a kasar nan, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Ya ce majalisar dattawa na ta kokari tare da assasa samar da kayan da jami'an tsaro ke bukata don samun ingantaccen aiki a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel