Babu inda zan je, zan ci gaba da shugabantar cibiyata - Dakataccen MD NSITF

Babu inda zan je, zan ci gaba da shugabantar cibiyata - Dakataccen MD NSITF

Hukumar Inshora ta Najeriya (NSITF) ta ce har yanzu hukumar za ta ci gaba da aikinta duk da dakatarwar da ministan aikin yi da kwadago, Chris Ngige ya yi mata.

A wata wasika mai kwanan wata 1 ga watan Yulin 2020 kuma aka mika ta ga Adebayo Somefun, manajan daraktan NSITF, Ngige ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar hukumar da Somefun ke jagoranta saboda badakalar wasu kudade da sauran laifuka.

An umarci Somefun da ya mika ragamar hukumar ga babban jami'in bayansa kuma ya fuskanci binciken yadda cibiyar ta yi aiki daga 2017 zuwa 2020.

Amma a martanin da ya fitar na ranar Alhamis, ya ce shugaban kasa bai bada wannan umarnin ba.

"Muna son sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bada umarnin ga hukumar NSITF ba kuma bai bada wannan sanarwar ba," takardar tace.

"Domin bayani, mun samu wasika daga mai girma ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, na cewa yana duba yadda aka kashe kudin hukumar kuma an dakatar da ita.

"Mun gano cewa abinda ministan yayi ya ci karo da umarnin shugaban kasar ta hannun sakataren gwamnatin tarayya inda yace babu ministan da aka yarjewa ya dakatar ko kora shugaban wata cibiya wacce shugaban kasar ya nada.

Babu inda zan je, zan ci gaba da shugabantar cibiyata - Dakataccen MD NSITF
Babu inda zan je, zan ci gaba da shugabantar cibiyata - Dakataccen MD NSITF. Hoto daga The Guardian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku zage damtse, ko mu saita muku hanya - Lawan ga Shugabannin tsaro

"Takardar ta ce ministocin su bi yadda ya dace ta hanyar bin kwamitin shugabanci na cibiyar har zuwa hannun sakataren gwamnatin tarayyar don daukar mataki.

"Muna mutunta yadda shugaban kasar yace a bi tsari kuma muna da tabbacin za mu samu kariya. Amma kuma a koda yaushe hukumar na bada damar a binciketa saboda babu abinda take boyewa," yace.

NSITF ta ce bata taba samun wasika ko wani korafi daga ministan ba, kuma za ta bayyana ko me ya faru ga jama'a da sauran hukumomi da suka kamata a lokacin da ya dace.

Ta kara da cewa, "Hukumar NSITF tana ayyukanta kamar yadda shugaban kasa ya bukata kuma tana kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankalinsu. Komai lafiya."

A wani al'amari makamancin hakan, Sale Mamman, ministan wutar lantarki a 2019 ya sallami shugabar NBET, Marilyn Ajimobi. Amma kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari sai ya hana hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel