Mutane 6879 sun warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

Mutane 6879 sun warke daga cutar korona a Najeriya - NCDC

- A yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya

- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 8,576, 1,444 suka warke kuma 126 suka kwanta dama

- Jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin Najeriya

- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 8,733, sai kuma mutum 2,501 da suka samu waraka, yayin da mutum 254 suka riga mu gidan gaskiya

Kusan watanni hudu bayan bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 na kasar da babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni.

Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.

Shugaban Hukumar NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban Hukumar NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 8,576, sai kuma mutum 1,444 da suka warke, bayan mutum 126 da suka kwanta dama.

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 20,244, sai kuma mutum 6,879 da suka samu waraka, yayin da mutum 518 suka riga mu gidan gaskiya.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, an yi wa mutum 115,760 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluma Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 12,847 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Da misalin karfe 11.33 na ranar Lahadi da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 436 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta dakatar da Giadom

Sabbin mutane 436 da cutar ta harba cikin jihohin 19 sun kasance kamar haka: Lagos (169), Oyo (52), Plateau (31), Imo (29), Kaduna (28), Ogun (23), Abuja (18), Enugu (18), Bauchi (17), Bayelsa (14), Rivers (8), Osun (6), Kano (6), Edo(5), Benue (5), Adamawa (3), Borno (2), Abia (1), Ekiti (1)

Har yanzu dai jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai jihar kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da suka warke daga cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da ta bulla:

Lagos (1,444),

Oyo (282),

Plateau (125),

Imo (21),

Kaduna (302),

Ogun (361),

Abuja-FCT (486),

Enugu (29),

Bauchi (324),

Bayelsa (14),

Rivers (391),

Osun (46),

Kano (712),

Edo(197),

Benue (15),

Adamawa (37),

Borno (362),

Ekiti (28),

Delta (124),

Gombe (246),

Katsina (233),

Jigawa (191),

Ebonyi (137),

Abia (93),

Nasarawa (88),

Kwara (122),

Bayelsa (29),

Sokoto (115),

Ondo (42),

Zamfara (71),

Kebbi (40),

Anambra (51),

Neja (37),

Akwa Ibom (43),

Yobe (45),

Taraba (10).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel