Kakakin Majalisar Gombe ya warke daga cutar Korona

Kakakin Majalisar Gombe ya warke daga cutar Korona

Kakakin majalisar dokoki na jihar Gombe, Ibrahim Abubakar Sadiq, ya warke daga cutar korona kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Haka zalika mataimakinsa, Siddi Buba, da wasu 'yan majalisar hudu sun samu waraka bayan kamuwa da cutar makonni biyu da suka gabata.

'Yan majalisar shida wanda a baya aka gano suna dauke da kwayoyin cutar ta Covid-19, sun killace kawunansu har na tsawon kwanaki 14.

A yanzu an tabbatar da sun tsarkaka daga cutar mai toshe kafofin numfashi.

Sai dai kakakin majalisar ya musanta zargin da ake yi na cewa an killace su ne a babban Otel din jihar Gombe.

Yana mai cewa, "kun samu labarin ba daidai ba, babu wani Otel da aka killace mu a cikinsa."

"Dukkanmu mun yanke shawarar killace kawunanmu a gida."

"Ba a kai mu wani Otel ba saboda wurin kasuwanci ne da mutane ke hada-hada."

Kakakin Majalisar Gombe, Muhammad Abubakar Sadiq
Kakakin Majalisar Gombe, Muhammad Abubakar Sadiq
Asali: Twitter

Yayin jaddada cewa cutar korona gaskiya ce, kakakin majalisar ya kuma yi gargadi a kan masu kyamatar mutanen da cutar ta harba bayan sun warke.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, makonni biyu da suka gabata ne sakamakon gwajin da aka yi wa 'yan majalisar ya nuna cewa shida daga cikinsu sun kamu da cutar korona.

Wata majiya da jaridar Daily Trust ta ruwaito ta bayyana cewa, an killace 'yan majalisar a cibiyoyin killacewa na jihar domin jinyarsu, yayin da aka dauki samfurin iyalansu domin gwaji.

KARANTA KUMA: APC ta fara gudanar da zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Edo

Hakazalika, kwamishanan ruwa na jihar, Yahaya Mijinyawa, ya kamu da cutar ta COVID-19. Kwamishanan ya bayyana hakan ne a kan shafinsa na Facebook.

Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayar ga duk makarraban gwamnatinsa da su gabatar da kansu domin ai musu gwajin cutar.

Gwamnan ya ba da umurnin ne bayan rasuwar wani Darekta a ofishin sakataren gwamnatin jihar, sakamakon kamuwa da cutar.

A ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni, sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya jagoranci ma'aikatan zuwa wajen gwajin domin a tabbatar da lafiyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel