Hukumar JAMB ta bayyana sunayen dalibai 13 da suka fi yin fice a jarabawar bana
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a da makarantu na gaba da sakandire wato JAMB, ta fitar da sunayen dalibai 13 da suka fi samun nasara a jarabawar bana.
Yayin taron fidda tsare-tsare da jadawalin da ta gudanar a makon da ya gabata, daliban da suka ciri tuta a jarabawar bana sun sami tsakanin 352 da 365.
Biyu daga cikinsu da suka fito daga jihar Anambra, sun fi kowa samun nasara, inda suka samu maki 365 da kuma 363.
Wani dalibi da ya fito daga jihar Edo, ya biyo bayansu da maki 359, yayin da wasu dalibai biyu da suka fito daga jihar Ekiti, sun sami maki 358 da 356 a mataki na hudu da na biyar a jere da juna.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, wasu dalibai biyu da suka fito daga jihar Delta, sun samu maki 359 da 352.

Asali: Twitter
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa
Sauran jihohin da suka samun nasarar fito da zakakuran dalibai sun hadar Ekiti, Ondo, Akwa Ibom, Kwara, Oyo da kuma Ogun.
Daga cikin daliban 13 da suka fi yin fice a jarabawar ta bana, biyu sun samu maki 359, wasu biyun sun samu 355 yayin da wasu daliban hudu suka samu 352.
Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin ya fitar.
Ga jerin sunayen daliban, jihohin da suka fito da kuma adadin makin da kowanensu ya samu:
1) Maduafokwa Egoagwuagwu Agnes -365
2) Nwobi Okwuchukwu David – 363
3) Ojuba Mezisashe Shalom – 359
3) Elikwu, Victor Chukwuemeka – 359
5) Adebola Oluwatobi Paul – 358
6) Gboyega Oluwatobiloba Enoch – 356
7) Ojo Samuel Oluwatobi – 355
7) Utulu, Jebose George – 355
9) Osom Akan Awesome – 353
10) Akakabota Fejiro Simeon – 352
10) Ogundele Favour Jesupemi – 352
10) Alatise Monsurah Bisola. – 352
10) Adelaja Oluwasemilore Daniel – 352
Dukkanin daliban sun nemi kwasa-kwasai a fannin nazarin karantun injiniya. Kama daga injiniyan masana'antu, gine-gine, kwamfuta, lantarki da sauransu.
Hudu suna neman shiga jami'ar Legas, biyu kuma jami'ar Covenant, jami'ar Obafemi Awolowa da kuma jami'ar Ilorin. Dalibi daya kuma yana neman samun shiga jami'ar Jihar Kwara.
Alkaluman Hukumar JAMB sun nuna cewa, dalibai 1,949,983 ne suka zana jarabawar a bana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng