Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa

Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da shugaban majalisar dattawa

- An gudanar da wani zaman ganawa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban majalisa dattawa, Sanata Ahmad Lawan

- Har zuwa lokacin da aka tattaro wannan rahoto, ba a san me shugabannin biyu suka tattauna a kai ba

- Masu rike da madafan iko na kasar sun gana da juna makonni biyu bayan da majalisar dattawa ta tafka muhawara kan kalubalen rashin tsaro da ya addabi kasar nan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, ya shiga bayan labule tare da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Mun samu rahoton cewa, shugaban kasar ya yi ganawar sirri ne tare da shugaban majalisar dattawa a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasar kan sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad, ya fitar a kan shafinsa na Twitter.

Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban majalisar dattawa
Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban majalisar dattawa
Asali: Twitter

Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban majalisar dattawa
Shugaba Buhari yayin karbar bakuncin shugaban majalisar dattawa
Asali: Twitter

Sai dai a yayin tattaro wannan rahoto, Legit.ng ba ta iya gano makasudin ganawar shugabannin biyu ba.

Sanarwar da hadimin shugaban kasar ya fitar ba ta fayyace dalilin ziyarar da shugaban majalisar ya kai wa ubangidansa ba.

Ganawar masu rike da madafan ikon kasar ta zo makonni biyu bayan da majalisar dattawa ta tafka muhawara kan kalubalen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

Majalisar a yayin zaman da ta gudanar a baya-bayan nan, ta sha alwashin kai wa shugaba Buhari takakkiya har fadarsa saboda yadda lamarin tsaro ya tabarbare a kasar.

KARANTA KUMA: Rundunar Sojin saman Najeriya ta yiwa 'yan Boko Haram ruwan wuta a Bula Bello da Ngoske

A bangare guda kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Agboola Ajayi, ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki a kasar ta APC.

Agboola ya sanar da cika bujensa da iska daga jam'iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Honarabul Agboola ya sanya hannu a takardar ficewarsa daga jam’iyyar APC a mazabarsa ta Ward 2, Apoi a karamar hukumar Ese-Odo ta jihar.

Mataimakin gwamnan ya kuma gaggauta karbar takardar zama dan jam’iyyar adawa ta PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel