Rundunar Sojin saman Najeriya ta yiwa 'yan Boko Haram ruwan wuta a Bula Bello da Ngoske

Rundunar Sojin saman Najeriya ta yiwa 'yan Boko Haram ruwan wuta a Bula Bello da Ngoske

Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kai wani hari kan mayakan Boko Haram a sansaninsu na Bula Bello da Ngoske da ke Dajin Sambisa a jihar Borno.

Rundunar LAFIYA DOLE mai yaki da masu tayar da kayar ba a Arewa maso Gabas, ta samu nasarar yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta da jiragenta na yaki.

An cimma wannan gagarumar nasara ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama ke yi babu sassauci tun bayan kaddamar da sabon aikin dakaru da aka yi wa lakabi da "Operation LONG REACH".

Operation LONG REACH wani sabon shiri ne da dakarun sojin suka fara gudanar da shi a ranar 16 ga watan Yuni domin kara kaimi da zage dantse wajen kawo karshen 'yan ta'adda a yankin.

Legit.ng ta samu rahoton hakan ne cikin wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni.

Rundunar Sojin saman Najeriya ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan wuta a Bula Bello da Ngoske
Rundunar Sojin saman Najeriya ta yi wa 'yan Boko Haram ruwan wuta a Bula Bello da Ngoske
Asali: Twitter

An samu nasarar kai harin ne biyo bayan samun wasu bayanan sirri da kuma leken asiri da rundunar sojin ta gudanar.

Rundunar sojin ta rika jefa wa mayakan Boko Haram bama-bamai gami da makami mai linzami wanda ya janyo mutuwar da dama daga cikinsu

Da yawa daga cikin mayakan Boko Haram sun ranta a na kare, sai dai da ya ke idan karar kwana ta zo babu makawa sai an tafi.

KARANTA KUMA: Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 300 a Kebbi

A cikin faifan bidiyon da rundunar sojin ta yada a zauren sada zumunta, an hangi mayakan na arcewa da kafafunsu, sai dai kafin su je ko ina an yi musu ruwan wuta da dole suka kwanta dama.

Legit.ng ta ruwaito cewa, rundunar Sojojin Saman Najeriya ta tarwatsa wani rukunin gidaje na wasu shugabannin Boko Haram tare da fatattakar wasu daga cikin mayaƙansu a Garin Maloma.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban jami'in sadarwa na rundunar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enoche, ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni.

Manjo Janar Enoche ya ce an samu nasara yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta da suka rage a Garin Maloma daf da dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Ya ce an gano mayakan Boko Haram sun fara fakewa a wasu rukunin gidaje masu shinge, inda suke shirye-shiryen tuggu da kuma horas da mabiyansu.

Rundunar sojin ta kai hari sansanin mayakan da ke Garin Maloma, wanda ya kasance babban tushe na sadarwarsu kuma yake iyaka da Dajin Sambisa.

Hakan ya sanya aka yi wa masu tayar da kayar bayan ruwan wuta daga sama wanda ya janyo musu mummunar asara mai girma.

An kuma sake yi wa ragowar mayakan ruwan wuta wadanda suka tsira daga harin na farko da dakarun suka kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel