Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 300 a Kebbi

Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 300 a Kebbi

Mun samu rahoton cewa kimanin gidaje 300 ne iska mai karfin gaske ta rusa sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka tamkar da bakin kwarya.

Rahotanni sun nuna cewar ruwan sama mai hadi da guguwa ya fi kamari ne yankin Badariya, Barikin 'Yan Sanda, Bayan-Kara da wasu sassan Gesse III a Birnin Kebbi.

Jaridar Herald ta ruwaito cewa, akalla gidaje 50 ne suka rushe a yankunan hudu da ke kwaryar Birnin Kebbi sakamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Juma'a.

Wani sashin wadanda ibtila’in ya shafa sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa wannan lamari ya yi matukar dugunzuma su.

A yayin da suke bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a yanzu, sun ce abu ne mai wahala a iya tantance girman ta'adin da ruwan saman mai hadi da iska mai karfi ya janyo.

Wani mazaunin daya daga cikin yankunan da tsautsayin ya auku, Malam Isyaku Muhammad, ya ce akalla gidaje fiye da hamsin sun ruguje sakamakon ruwan saman da aka shatata.

Yana mai cewa, "ina ganin ba kuskure idan har mutum ya ce gidaje fiye da hamsin sun rushe a sassa daban-daban na jihar nan."

Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 300 a Kebbi
Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 300 a Kebbi
Asali: Twitter

"Mun rungumi wannan lamari da ya auku a matsayin kaddara daga Allah, wanda ke yin abin da Ya so a lokacin da Ya so, ba tare da neman shawarar kowa ba," inji Muhammad.

Daga bisani ya roki gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki domin rage musu radadin ibtila'in da ya auku.

A nasa bangaren, Mista Isaac Musa, daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya ce ruwan saman kamar da bakin kwarya ya fara sauka ne da yamma, inda ya rusa gidaje da yawa "ba kawai a nan Badariya ba har ma da wasu wurare."

Mista Isaac ya yi kira ga gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma mawadata da su tallafawa musu da matsugunan da za su zauna.

Cikin hanzarin nuna kulawa, gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, ya kai ziyara yankunan da lamarin ya shafa kuma ya jajantawa mutanen da ibtila'in ya jefa cikin halin kakanikayi.

KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aikin sai baba-ta-gani da suka shiga

A wata sanarwa da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kebbi, Abubakar Mu'azu Dankingari ya fitar a ranar Asabar, ya ce gwamnan ya kai ziyarar ne ranar Juma'a da Yamma.

A cewarsa, gwamnan ya kai ziyarar gani da ido yankunan ne domin tantance girman asarar da ibtila'in ya janyo a unguwar Badariya.

Gwamna Bagudu ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa da kayayyakin agaji.

Ya kuma nemi wadanda lamarin ya shafa da su dauki dangana tare da rungumar lamarin a matsayin kaddara tare da yin addu'ar Allah ya kawo musu sauki.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, gine-gine da dama da turakun wutar lantrki sun zube sakamakon guguwar da auku musamman a yankin Badariya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel