Cika shekaru 45: Shugaba Buhari ya aika da sakon taya murna na musamman ga Yahaya Bello

Cika shekaru 45: Shugaba Buhari ya aika da sakon taya murna na musamman ga Yahaya Bello

- Shugaba Buhari ya taya gwamnan jihar Kogi murnar cikar sa shekaru 45 da haihuwa

- Da yake taya sa murna, shugaban na Najeriya ya aika masa da sakon fatan alheri a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni

- A sakon na taya murna, Buhari ya bayyana gwamna Yahaya Bello a matsayin gwarzo mai aminci da biyayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sako na musamman zuwa ga gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, a yayin murnar cikar sa shekaru 45 da haihuwa.

Buhari ya bayyana gwamnan jihar Kogi a matsayin garkuwar ta aminci da biyayya.

Shugaban kasar ya jinjinawa kwazon da ya jajirci wajen kawo ci gaban jam’iyyarsu ta APC tun daga tushenta.

Sakon taya murna na shugaban kasan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga Yuni, ta hannun hadiminsa na sabuwar hanyar sadarwa, Bashir Ahmad.

Shugaba Buhari tare da Yahaya Bello a fadar shugaban kasa
Shugaba Buhari tare da Yahaya Bello a fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

KARANTA KUMA: Guguwa ta hallaka mutum shida, ta rusa gidaje 600 a Kano

"Ina alfahari da kai da kuma kwazon ka gami da hidimar da ka ke yi wa jam'iyyarmu a kowane lokaci. Kuma kai mutum ne dan jam'iyya na gaske da ya cancanci a taya sa murna," in ji shi.

“Yayin da kake murnar wannan biki na farin ciki, ina taya ka murna a madadina da iyalina yayin da ka cika shekaru 45 da haihuwa cikin koshin lafiya."

"Ina rokon Allah ya albarkace ka da koshin lafiya da tsawon rai domin ci gaba da yi wa al'ummar jiharka hidima."

A cewar shugaba Buhari, gwamnan da ke yi wa mutanen Kogi aiki tun a farkon rayuwarsa ta matashi, zai bashi wata dama ta musamman don yin aiki da ƙarfin tunani da harsashi.

Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin arewa ta yi taro a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni domin duba yanayin rashin tsaro da ya addabi yankin.

Taron da aka yi ta yanar gizo wanda shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong ya jagoranta, ya jajanta a kan karuwar rashin tsaro a yankin arewa.

A yayin taron, gwamnonin sun fara zantawa a kan matakan dauka a kan lamarin da ya ke ci musu tuwo a kwarya.

Daga cikin matakan, sun amince da kafa kwamitin kula da tsaro a arewa wanda zai dinga duba al'amuran tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, shi aka nada shugaban kwamitin yayin da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara da takwaransa na Gombe, Muhammad Yahaya suka zama mambobi.

Daya kwamitin ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, Abubakar Bello na Neja da Aminu Tambuwal na Sakkwato.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel