WHO ta ayyana Najeriya ta yi sallama da cutar shan inna

WHO ta ayyana Najeriya ta yi sallama da cutar shan inna

A ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ayyana cewa Najeriya ta yi sallama da cutar shan inna yayin da cutar ta cika bujenta da iska.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta wallafa kan shafinta na dandalin sada zumunta wanda ake kira Twitter.

WHO ta ce a halin yanzu kasashe biyu ne kacal a duniya suke ci gaba da fama da annobar cutar, wanda ya nuna sauran kiris a cimma burin ganin bayan cutar a doron kasa.

An ce Najeriya ta sami wannan matsayi ne bayan kammala takaddun wanda Hukumar ba da Takaddun Kula da Yankin Afirka ta amince da shi don kawar da cutar shan inna.

An ruwaito cewa Najeriya ta cimma wannan mataki na tsarkaka daga cutar shan inna, bayan da ta kammala shigar da duk wasu bayanai da Hukumar tantance kasashen Afrika ta amince da su.

Yayin da Buhari ya karbi lambar yabo ta gwarzon yaki da cutar shan inna a 2018
Yayin da Buhari ya karbi lambar yabo ta gwarzon yaki da cutar shan inna a 2018
Asali: Twitter

Ta ce, "tsagwaran himma da kokari sun taka rawar gani wajen bai wa Najeriya damar ficewa daga ajin kasashe masu fama da annobar domin tabbatar da nahiyar Afrika baki daya ta tsarkaka."

"A yanzu dole mu hada karfi da karfe wajen goyon bayan yunkurin da kasar Pakistan da Afghanistan su ke yi domin ganin sun bi sahun samun tsarki daga cutar a duniya."

KARANTA KUMA: Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka

Da yake martani a kan lamarin, Kakakin Hukumar Kula da Kiwon Lafiya NPHCDA, Mohammad Ohitoto, ya shaidawa jaridar Punch cewa 'yan Najeriya da hukumar sun yi farin ciki matuka.

Idan ba a manta ba, a ranar 15 ga watan Nuwamban 2018 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi lambar yabo da gwarzon yaki da cutar korona a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Sanarwar hakan ta na kunshe cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina ya wallafa kan shafinsa na Facebook.

Legit.ng ta ruwaito cewa, babban daraktan kamfanin Novartis, Vas Narasimhan, ya bayyana Pneumonia, zazzabin cizon sauro da gudawa a matsayin manyan cututtuka uku da suka fi kashe yara a Afirka.

Narasimhan wanda shi ne shugaban kamfanin hada magunguna na Novartis ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin sakon sa na Ranar Yaran Afirka ta bana.

Ya yi kira ga shugabannin Afirka da su dauki matakin kare kananan yara daga wadannan cututtukan.

A cewar Narasimhan, ana iya samun mace-macen kananan yara sau takwas a Afirka wadanda basu haura shekaru biyar ba a duniya gabanin a samu mutuwar guda a nahiyar Turai.

Ya ce cutar sanyi dake kama hunhu da hakarkari wato ‘Pneumonia’, ta fi kowace cutar saurin kashe kananan yara a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel