Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima

Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima

Bayan majalisar dinkin duniya ta ware ranar 19 ga watan Yunin duk shekara don yaki da cin zarafi, wata baiwar Allah da ta bukaci a boye sunanta ta shaida wa BBC cewa "'yan Boko Haram sun ci zarafinmu inda suka dinga lalata da mu."

Matashiyar ta sanar da cewa wannan lamarin ya auku ne a lokacin da mayakan ta'addancin Boko Haram suka kai hari garinsu.

A cewarta, "Mayakan sun shigo garinmu a ranar wata Talata suna kabbara har suka karbe garin. Sun kashe dukkan maza sannan suka kada matan."

Ta kara da cewa "ranar wata Talata sai 'yan Boko Haram suka shigo garinmu suna kabbara inda suka karbe garin suka kuma kashe duk maza sannan sai suka kada duk mata zuwa daji bayan sun kone garin.

"A wannan ranar kawuna ya zo wanda kanin mahaifina ne, ya ce in bishi na zama ganimar yaki. Daga nan ya tafi dani ya dinga saduwa da ni."

Matashiyar ta ci gaba da cewa, "Daga bisani aka samu daya daga cikin wadanda suka kashe mahaifina aka aura masa ni.

"Na samu guduwa daga hannunsa a wani dare da misalin karfe daya saboda a wannan lokacin suna bacci."

Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima
Yadda kawuna dan Boko Haram ya dinga lalata dani a matsayin ganima. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harbi a Aso Rock: An sauya wa dogarai 20 na Buhari wurin aiki

Kamar yadda matashiyar ta bayyana, duk da tserewar da suka yi daga hannun 'yan Boko Haram, tana fuskantar tsangwama da cin zarafi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Bama.

Ta kara da cewa, "Duk wurin da muka bi ko muka zauna a sansanin, sai a dinga nuna mu ana cewa ga matan 'yan Boko Haram.

"A gaskiya ba zan taba yafewa ba a kan abinda Boko Haram ta yi min ballantana kawuna wanda ya dinga lalata da ni. Allah ya isar min."

Daga bisani, matashiyar ta samu komawa makarantar Boko inda tace tana fatan zaman sojar sama don yakar Boko Haram.

"Burina a halin yanzu shine zama sojan sama domin in yi amfani da jirgi don wargaza Boko Haram. Ina fatan ganin bayan Boko Haram a Najeriya," in ji matashiyar.

A halin yanzu tana makaranta sannan tana koyon sana'ar dinki a wata cibiyar agaji ga masu gudun hijira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng