Dawo da zirga-zirgar jiragen saman cikin gida ba za ta yiwu ba a ranar 21 ga watan Yuni - NCAA

Dawo da zirga-zirgar jiragen saman cikin gida ba za ta yiwu ba a ranar 21 ga watan Yuni - NCAA

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa jigilar jiragen saman cikin gida ba za ta yiwu a dawo ita ba a ranar 21 ga Yuni, sabanin yadda ta zayyana a baya.

A baya dai kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona, ya ba da amicewarsa ta a dawo da jigilar jiragen saman cikin gida daga ranar 21 ga watan Yuni.

Sai dai a ranar Alhamis, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, yayin ganawa da kwamitin ya ce dawo da zirga-zirga jiragen saman cikin gida a wannan rana ba za ta yiwu ba.

Saboda haka ya nemi a jingine maganar domin kuwa a yanzu babu yiwuwar hakan duba da shirye-shiryen da suke yi bai kammala ba.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
Asali: Twitter

Ministan ya ce har kawo yanzu akwai shirye-shiryen da dole sai an kammalu su gabanin a iya dawo da jigilar jiragen, lamarin da ya ce dawo da ita a ranar 21 ga watan Yunin akwai hatsari.

Ya yi bayanin cewa, za a sanya sabuwar rana ta dawo da jigilar jiragen bayan hukumar sufurin jiragen sama (NCAA) ta gabatar da rahoton kan matakin shirinta da za a yi bitarsa a makon gobe.

Da yake jawabi dangane da shirin, Ministan wanda Shugaban Hukumar NCAA ya wakilta, Kyaftin Musa Nuhu, ya yi karin haske kan dalilan da suka sa dawo da jigilar ba za ta yiwu ba.

Ya kara da cewa NCAA za ta fitar da takamaimiyar ranar da za a dawo da jigilar bayan ta kammala shirinta da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki.

KARANTA KUMA: Kwarankwasa ta hallaka jami'an FRSC 3 a Ogun

Bayan da gwamnatin Tarayya ta sassauta dokar kulle tare da ba da umarnin dawo da jigilar jiragen saman cikin gida, ta fidda sunayen filayen jiragen sama biyar da za a bude a kasar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban hukumar sufurin jiragen sama, shi ne ya sanar da hakan cikin wata wasika mai kwanan dauke da watan ranar 1 ga Yunin 2020.

Kamar yadda wasikar da ya rubuta ta bayyana, filayen jiragen saman da za a bude su ne:

1. Filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

2. Filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

3. Filin tashi da saukar jiragen saman da ke Fatakwal, Omagwa a jihar Ribas.

4. Filin dauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano.

5. Filin sauka da tashin jiragen sama na Sam Mbakwe da ke Owerri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel