Jiragen Sojoji sun yi wa mayakan Boko Haram ruwan wuta a garin Maloma
Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta tarwatsa wani rukunin gidaje na wasu shugabannin 'yan ta'adda na Boko Haram tare da fatattaki wasu daga cikin mayaƙansu a Garin Maloma.
Rundunar LAFIYA DOLE mai yaki da masu tayara da kayar ba a Arewa maso Gabas, ta samu nasara yi wa 'yan ta'addan ruwan wuta da suka rage a Garin Maloma daf da dajin Sambisa da ke jihar Borno.
An cimma hakan ne ta hanyar ka hare-hare da jiragen sama babu sassauci yayin da aka kaddamar da sabon aikin dakaru da a aka yi wa lakabi da "Operation LONG REACH".
Operation LONG REACH wani sabon shiri ne da dakarun sojin kasar suka fara gudanar da shi a ranar 16 ga watan Yuni domin kara kaimi da zage dantsen kawo karshen 'yan ta'adda a yankin
Mun samu rahoton hakan ne cikin wata sanarwa da Babban jami'in sadarwa na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar John Enoche, ya fitar a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni.

Asali: Facebook
Rundunar sojin ta kai hari sansanin 'Yan Boko Haram da ke Gari Maloma, wanda ya kasance babban tushe na sadarwa a tsakanin mayaka wanda ke iyaka da Dajin Sambisa.
An samu nasarar kai harin ne biyo bayan samun wasu bayanan sirri da kuma leken asiri da rundunar sojin ta gudanar.
KARANTA KUMA: Binciken kashe-kashen kudi: Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da wasu
An gano cewa mayakan Boko Haram sun fara fakewa a wasu rukunin gidaje masu shinge, inda suke shirye-shiryen tuggu da kuma horas da mabiyansu.
Yayin shawagi da binciken na leken asiri da wasu jiragen saman dakaru suka gudanar, an gano mayakan Boko Haram su na kai-komo da sintiri a rukunin gidajen.
Hakan ya sanya aka yi wa masu tayar da kayar bayan ruwan wuta daga sama wanda ya janyo musu mummunar asara da kuma mutuwar da dama daga cikinsu
An kuma sake yi wa ragowar mayakan ruwan wuta wadanda suka tsira daga harin na farko da dakarun suka kai.
Shugaban hafsan sojin sama na kasa, Air Marshal Sadique Abubakar, ya yaba da kwazon dakarun tare da umartar su da kara kaimi domin cimma nasara a kan masu makiyan kasar nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng