Binciken kashe-kashen kudi: Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da wasu

Binciken kashe-kashen kudi: Majalisa ta gayyaci shugabannin NNPC, CBN, FIRS, da wasu

Majalisar Wakilai ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da kuma Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kolo Kyari.

Haka kuma Majalisar ta gayyaci Shugaban Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali, domin su yi bayani filla-filla game da duk wani shige-da-ficen kudi a ma'aikatun da suke jagoranta.

An gayyaci shugabannin hukumomin gwamnatin tarayyar ne saboda sun ki bayar da bayani yayin da ofishin Odita-Janar na Tarayya ya nuna rashin gamsuwa da yadda suke kashe kudade.

Zauren Majalisar wakilai
Zauren Majalisar wakilai
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shugabannin hukumomin gwamnatin sun ki yi wa ofishin Odita-Janar na Tarayya bayanin yadda suke kashe kudade duk da ya nemi bukatar hakan.

Sauran wadanda ake sa ran za su bayyana a gaban kwamitin bin diddigin kudi na majalisar sun hadar da:

Shugaban Hukumar FIRS; Mohammed Nami

Shugaban Hukumar da ke sa ido kan kayyade albashin manyan jami'an gwamnati; Elias Mbam;

Darektan Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya DPR; Sarki Auwal;

Babban Sakataren Hukumar kayyade farashin man fetur PPRA, Abdulkadir Saidu;

Shugaban Hukumar Zuba Jari ta Najeriya (NSIA); Uche Orji;

Shugaban Kamfanin sarrafa iskar gas na NLNG, Tony Attah;

Shugabannin Hukumar Kula da Shirin gwamnatin Tarayya na rage radadin janye tallafin man fetur wato Sure-P;

Manyan Sakatarorin dindindin na Ma'aikatar Kudi ta Tarayya; Dr Mahmoud Isa-Dutse; Dr Muhammed Dikwa; Mr Ernest Umakhir.

KARANTA KUMA: Ikirarin Maryam Abacha na cewa mijinta bai yi sata ba ya girgiza ni - Itse Sagay

Babban Sakataren dindindin na Ma'aikatar hako Ma'adanai ta Tarayya; Dr. Abdulkadri Mu'azu;

Shugaban Hukumar hako Ma'adanai; Engr. Obadiah Simon Nkom.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban kwamitin bin diddigin kudi na majalisar, Wole Oke, shi ne ya gabatar da takardun goron gayyatar manyan jami'an gwamnati da har yanzu ba su amsa ba.

Mista Oke yayin zaman tattaunawa kan binciken kashe-kashen kudi da Odita-Janar na tarayya ya gabatar, ya gargaɗi manyan jami'an gwamnatin da aka gayyata da su tabbatar sun yi biyayya.

A yayin zaman ne Akanta-Janar na kasa, Ahmed Idris, ya yi bita tare da yi wa kwamitin majalisar bayani dalla-dalla dangane da yadda aka kashe kudi a ofishinsa kamar yadda Odita-Janar ya nema.

Majalisar za ta wallafa rahoto a cikin manyan jaridu uku na kasar dangane da yadda za ta kaya da duk manyan jami'an gwamnatin da ta aikawa da goron gayyata.

Ta ce "'Yan Najeriya sun cancanci sanin abin da ya ke faruwa da kudadensu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel