Ikirarin Maryam Abacha na cewa mijinta bai yi sata ba ya girgiza ni - Itse Sagay

Ikirarin Maryam Abacha na cewa mijinta bai yi sata ba ya girgiza ni - Itse Sagay

Shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, yiwa uwargidan tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha martani.

Farfesa Sagay ya ce ya girgiza matuka da ikirarin cewa marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja bai saci kudi daga asusun gwamnatin Najeriya ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, duk yadda ake ci gaba da dawowa da Najeriya kudaden da Abacha ya yi ruf da ciki a kansu, uwargidansa, Maryam, ta dage a kan cewa mijinta bai yi satar ko asi ba.

A baya bayan nan Maryam ta ce, "ana karyar an gano kudaden kuma an dawo da su, nawa ne kudin da aka dawo da su bayan shekaru 22 da mutuwarsa?

"Abin kunya ne ake yi wa mamaci karya, abin kunya ne ake yi wa shugaba karya.

"Idan ya aikata ba daidai ba, Allah ya sani. Idan wasu mutane ne ma suke yi masa sharri, lokaci zai nuna.

"Sai sun gurfana a kan gwuiwowinsu kamar yadda yanzu Amurka ta gurfana. Duk wani mugu sai ya durkushe kamar yadda annobar korona ta durkusar da dukkan duniya."

Shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay
Shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay
Asali: Twitter

Maryam ta bayyana hakan ne a matsayin martani ga labaran da ake yadawa a kan kudaden da ake dawowa Najeriya dasu, wadanda aka alakanta cewa mijinta ne ya yi satar su.

Wannan ikirari ya dugunzuma hadimin shugaban kasar, inda yayin ganawa da manema labarai ya bayyana mamakinsa da cewa ta ya za ayi a danne gaskiya bayan ta bayyana karara a zahiri.

Ya ce ikirarin da Maryam ta yi ya gigita shi domin kuwa babu ta yadda za a yi a ce marigayi Abacha bai yi handama da babakere ba a lokacin da ya mulki kasar nan.

Sagay yayi mamaki idan duk kudaden da aka dawo da su daga ƙasashen waje an karbo su ne daga cikin albashin da Abacha ya tara ko kuma hannayen jarin da ya zuba a harkokin kasuwanci.

KARANTA KUMA: Bude gidajen kallon kwallo ya ci karo da umarnin gwamnatin tarayya - Boss Mustapha

Yana cewa: "Ni yanzu na kasa fahimtar wannan lamari domin kuwa ban taba tsammanin wani zai iya fitowa yayi jayayya haka ba."

"To yanzu daga ina kudaden da ake dawowa da Najeriya suke fitowa kenan?" Sagay ya yi tambaya cikin mamaki.

Legit.ng ta ruwaito cewa, matar marigayi tsohon shugaban kasar ta ce abin kunya ne ake yi wa mamaci karya.

Yayin wata hira da aka yi da ita a Kano domin tunawa da cika shekaru 22 da mutuwar Abacha, Maryam ta ce da sannu gaskiya za ta fito a kan kudaden da ake dorawa mijinta laifin sacewa.

Hajiya Maryam ta zargi manyan mutanen Kano da cin amanar mijinta da ya mutu a shekarar 1998, "duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar da kasa baki daya."

Tun bayar mutuwarsa a shekarar 1998 ake dawowa da Najeriya makudan kudaden da ya jibge a bankunan nahiyar Turai da Amurka, ya ajiye mafi yawancin kudaden ne da sunan 'ya'yansa.

Ko a makon jiya sai da tsohon dogarin da ke kula da tsaron tsohon shugaban kasa Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya sake kare mai gidansa game da zargin da ake yi masa na satar dukiyar gwamnati.

Al-Mustapha ya ce gwamnatin Abacha ta tuntubi sarakunan Arewa da na Kudu da duk wasu manya da ake ji da su a kasar kafin ya boye biliyoyin kudin da yanzu ake kira ‘satar Abacha.’

Al-Mustapha ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da gidan jaridar BBC Hausa, inda ya ce dole ta sa Janar Sani Abacha ya rika boye biliyoyin kudi a kasar waje domin ya hararo cewa za a makawa Najeriya takunkumi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel