Buhari ya umarci Ministoci hudu da su fito da wani sabon salo da zai magance matsalar rashin tsaro

Buhari ya umarci Ministoci hudu da su fito da wani sabon salo da zai magance matsalar rashin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministoci hudu da ke kula da harkokin tsaro su fito da wasu sabbin dabaru da nufin shawo kan matsalolin tsaro da ke fuskantar kasar.

A jiya ne shugaban kasar ya kuma aike da shugabannin tsaro, karkashin jagorancin mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, zuwa jihar Katsina.

Shugaban kasar ya aike da tawagar tsaron ne biyo bayan samun tashe-tashen hankula gami da rashin tsaro a jihar, domin nemo mafita mai dorewa.

Sauran 'yan tawagar sun hadar da Sifeto Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, Darekta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi da kuma shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, Ahmed Rufa'i.

A Larabar da ta gabata ne dai Ministocin hudu da akalar tsaron kasar ke hannunsu suka gana a birnin Abuja, da nufin sauke nauyin da shugaban kasa ya rataya a wuyansu.

Buhari ya nemi 'yan majalisar gwamnatinsa da su zage dantse wajen tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi jihar Kastina da sauran jihohin da ke Arewa maso Yamma gaba daya.

Buhari yayin ganawa da shugabannin tsaro
Hakkin Mallakar Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Buhari yayin ganawa da shugabannin tsaro Hakkin Mallakar Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Ci gaba da tabarbarewar tsaro a bayan nan ta janyo hankalin kusan duk bangarori na siyasa, addini, da shugabannin al'umma ke kiran gwamnati a kan ta yi hanzarin magance masu tayar da zaune tsaye a kasar.

A sakamakon hakan ne dai Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi Allah wadai da kisan gillar da ‘yan Boko Haram da 'yan bindiga suke yi a fadin kasar.

KARANTA KUMA: Cutar Pneumonia, amai da gudawa da zazzabin cizon sauro sun fi kashe kananan yara a Afirka

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, ministocin hudu da Buhari ya umarta za su tunkari matsalolin rashin tsaro a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato da kuma sauran sassan kasar nan.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro ta fitar ta bayyana cewa, ministocin hudu sun yi wata ganawa ta tsawon awanni uku domin tumke damarar sauke nauyin da shugaba Buhari ya rataya musu.

Ministocin hudu sun hadar da na Ma'aikatar Tsaro; Bashir Salihi Magashi da Ministan Harkokin 'Yan Sanda; Muhammad Maigari Dingyadi.

Sai kuma Ministan Harkokin Cikin Gida; Rauf Aregbesola da kuma Ministan Labarai da Al'adu; Lai Mohammed.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel