Bude gidajen kallon kwallo ya ci karo da umarnin gwamnatin tarayya - Boss Mustapha

Bude gidajen kallon kwallo ya ci karo da umarnin gwamnatin tarayya - Boss Mustapha

Lallai likafar ci gaba da cin kasuwa ta bude ga masu gidajen kallon kwallo a wasu sassa da dama a fadin Najeriya, inda a ranar Laraba suka haska wasannin gasar Firimiya da aka buga.

Sai dai fa wannan lamari ya na cin karo da umarnin da kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona (PTF) ya gindaya na hana bude gidajen kallon kwallo a fadin kasar.

Gasar Firmiyar Ingila wadda ta ke da dumbin masoya a Najeriya, an ci gaba da gudanar da ita a ranar Laraba tun bayan dakatar da ita a ranar 13 ga watan Maris saboda annobar korona.

Wasu masu gidajen kallon kwallo a jihohin Legas, Ondo, Ogun, da Ekiti, sun bayyana farin cikinsu matuka sakamakon ci gaba da gasar yayin zantawa da manema labarai na jaridar The Punch.

Sun kuma bayyana shirye-shiryensu na kiyaye matakan bayar da tazara da zaman nesa-nesa da juna yayin haska wasanni a wuraren da suke neman na abinci.

Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona (PTF)
Hakkin Mallakar Hoto; Fadar Shugaban Kasa
Kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona (PTF) Hakkin Mallakar Hoto; Fadar Shugaban Kasa
Asali: Twitter

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga bakin shugaban PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya yi gargadi a kan haramcin bude gidajen kallon kwallon kafa.

Wannan sanarwa ta rushe murnar da wasu masu gidajen kallon kwallon ke yi, inda suka ci gaba da lissafin irin asarar da suke yi tun daga lokacin da aka dakatar da duk wasanni a duniya.

KARANTA KUMA: Buhari ya umarci Ministoci hudu da su fito da wani sabon salo da zai magance matsalar rashin tsaro

"Mun samu cewa wasu jihohi na tunanin ba da damar sake bude makarantu, gidajen kallon kwallo da sauran wurare masu tara jama'a," inji Sakataren Gwamnatin a sanarwar da ya yi a ranar Litinin.

"Muna sake jaddada cewa, yin hakan akwai babban hatsari kuma muna gargadin duk masu wannan yunkuri su jingine shi a gefe saboda ya na cin karo da sharudan da muka shata."

Sai dai wani bincike ya nuna cewa gidajen kallon kwallo da dama sun ci kasuwa a ranar Laraba, 17 ga Yuni, inda suka haska wasannin farko da aka fafata bayan an ci gaba da gasar Firimiya.

Da yawa daga cikin masoya kwallon kafa da suka halarci gidajen kallon basu sanya takunkumin rufe fuska ba ballanta su bayar da wata tazara a tsakaninsu.

Baya ga rashin kiyaye dokar nesa-nesa da juna, babu wuraren ta aka tanada domin wanke hannaye a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin wanke hannu (Sanitizer).

Legit.ng ta fahimci cewa, gidajen kallon kwallo sun cika makil yayin da aka buga wasanni tsakanin Aston Villa da Sheffield United da kuma wanda aka buga tsakanin Arsenal da Manchester City a ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel