Sarkin Daura ya sauya fasalin majalisar hakimai

Sarkin Daura ya sauya fasalin majalisar hakimai

Mai martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Farouk, ya gudanar da sauye-sauye ga wasu Hakimansa domin inganta zaman lafiya da hadin kai a masarautar.

Kakakin masarautar, Malam Usman Ibrahim, shi ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba, a fadar Daura.

Malam Ibrahim ya ce an daga likafar Sarkin Tsaftar Daura, Alhaji Lawal Usman zuwa mukamin Kauran Daura, wanda a yanzu ya shiga cikin sahun masu zaben sarki a masarautar.

Haka kuma an bai wa Sarkin Sudan, Alhaji Yusuf Nalado, kujerar babban mashawarci na musamman ga Sarkin Daura.

A cewar kakakin Masarautar, Sarkin na Daura ya nemi hakiman da aka daga likafarsu da su jajirce wajen yin aiki na aminci da adalci sannan kuma su kawo zaman lafiya da hadin kai.

Sarkin Daura; Dakta Umar Farouk
Sarkin Daura; Dakta Umar Farouk
Asali: Twitter

Sarkin ya kuma hori 'yan majalisar da su dage wajen kwarara addu'o'i na neman zaman lafiya da hadin kai a daukacin jihar Katsina da kuma kasa baki daya.

A yayin haka Sarkin ya kuma yi kira ga al'umma da su tabbatar sun dabi'antu da juriya da hakuri bisa koyarwar Manzon Tsira, Annabi Muhammad (Sallahu Alaihi Wassalama).

Yana mai cewa, "cikakkaen mai imani shi ne wanda al'umma suka aminta da zama tare da shi, kuma ya ke mayar da kauna da soyayya a yayin da aka nuna masa kiyayya."

KARANTA KUMA: Majalisar wakilai ta ki amincewa da an batar da N186bn a shirin ciyar da dalibai

Babu shakka jihar Katsina na ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a baya bayan nan, inda ake zargin wasu daga cikin masu rawani na da hannu a lamarin.

Kwanan nan ne Malam Garba Shehu, hadimin shugaba Muhammadu Buhari, ya fito karara ya bayyana cewa, wasu sarakunan gargajiya na da hadin baki da masu tayar da zaune a jihar Katsina.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani shiri na' Sunrise Daily' wanda gidan Talbijin na Channels ya saba yadawa.

Mallam Shehu ya ce wasu sarakunan gargajiya su na bai wa 'yan bindiga wurin fakewa yayin da jami'an tsaro suke kai hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel