Majalisar wakilai ta ki amincewa da an batar da N186bn a shirin ciyar da dalibai

Majalisar wakilai ta ki amincewa da an batar da N186bn a shirin ciyar da dalibai

Majalisar Wakilai ta fusata a kan Naira biliyan 186 da aka yi ikirarin batarwa a shirin ciyar da dalibai na Gwamnatin Tarayya tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

Majalisar ta hau kujerar naki tare da kaddamar da bincike kan ikirarin da ake yi na batar da wannan makudan kudi a shirin Gwamnatin Tarayya na ciyar da dalibai daga shekarar 2016.

Shugaban kwamitin bin diddigin kashe-kashen kudi, Honarabul Busayo Oluwole Oke da sauran mambobin kwamitin, sun titsiye jami’ar shirin ciyar da daliban, Sinkaye Temitope.

Majalisar ta bukaci bayanai filla-filla yayin da Misis Temitope ta gurfana a gaban kwamitin majalisar tare da babban jami'in gudanar da shirin, Mr Iowa Apera, a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

Yayin da ta ke jawabi, Temitope ta ce shirin ciyar da dalibai wanda aka fara shi tun a shekarar 2016, ya lakume naira biliyan 186 kawo yanzu.

Zauren Majalisar wakilai
Zauren Majalisar wakilai
Asali: Facebook

Ta bayyana cewa, an kaddamar da shirin ne tun gabanin kafa sabuwar Ma'aikatar Jinkai da Ci gaban Al'umma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a bara.

Temitope ta bayyana cewa, an kashe Naira biliyan 63.2 a 2018, sai biliyan 32.2 a 2019, yayin da aka batar da Naira biliyan 124.4 a bana.

Yayin da yake mayar da martani a fusace da nuna rashin yarda, Honarabul Busayo ya ce sam ‘yan majalisar ba su gamsu da yadda aka kashe kudaden ba.

KARANTA KUMA: Buhari zai halarci taron hadin kan China da Afrika

Kwamitin ya kuma bukaci a yi masa cikakken bayanin yadda aka kashe wasu Naira biliyan 64 daga cikin naira biliyan 186 na kudaden da ake ikirarin an kashe wajen ciyar da daliban.

Majalisar ta kuma nuna rashin aminci kan wata takarda da ta nuna cewa an ciyo bashin wasu makudan kudi wajen aiwatar da shirin na ciyar da daliban.

Bashin da majalisar ta nuna rashin yarda a kai sun hadar da Dala miliyan 400 daga Bankin Duniya, Dala miliyan 321 daga kudaden Abacha da kuma Dala miliyan 400 da aka karbo daga asusun gwamnati na equity.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, 'yan kwamitin za su bi takardun daki-daki domin tabbatar da ko an kwatanta gaskiya yayin kashe kudaden.

Sauran'yan kwamitin da suka nuna rashin gamsuwa game da batun kashe kudin sun hadar da Ifeanyi Chudi Momah (Anambra- APGA), da Miriam Onuoha (Imo-APC).

Sun yi babatu da cewa, har yanzu al'ummar yankunan da suke wakilta ba su ma san da wani shirin ciyar da dalibai ballanta su amfana da shi.

Musamman Momah, ya bayyana bacin rai matuka yayin da takardar ta nuna cewa dalibai 200,000 sun ci moriyar shirin ciyarwa da aka gudanar a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel