Buhari zai halarci taron hadin kan China da Afrika

Buhari zai halarci taron hadin kan China da Afrika

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Laraba, 17 ga watan Yuni, zai halarci taron hadin kan China da kasashen Afrika na musamman da za a gudanar.

Za a gudanar da taron ne daga nesa ta hanyar bidiyo kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Shugaba Buhari zai halarci taron ne domin tumke damarar hadin kan yaki da cutar korona da za a gudanar da misalin karfe 12.30 na rana.

Shugaban China, Xi Jinping, shi ne zai jagoranci taron hadin kan kasar Sin da kasashen nahiyar Afrika tun daga can fadar gwamnatinsa da ke birnin Beijing.

Gwamnatin China ce ta nemi a gudanar da taron a yanzu tare da hadin gwiwar kungiyar kasashen Afrika ta AU da kuma kasar Senegal wadda ta kasance uban gayya ta taron.

Buhari yayin da ya kai ziyara kasar China
Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Buhari yayin da ya kai ziyara kasar China Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Jerin wadanda za su halarci taron domin amsa goron gayyata sun hadar da shugabannin kasashen Afirka ciki har da mambobin kungiyar Majalisar Tarayyar Afirka.

Sauran masu halartar babban taron sun hadar da shugabannin kungiyoyi da gwamnatoci a nahiyyar Afrika da kuma Shugaban hukumar kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat.

KARANTA KUMA: Macen Macen Kano: Kashi 15% ne kadai suke da alaka da cutar korona - Ganduje

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres da kuma Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesu, za su halarci taron a matsayin manyan baki na musamman.

A sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, ta ce"China ta nuna matukar muhimmanci ga huldar abokantaka ta hadin gwiwa da Afrika, kuma a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Afirka don gina makomar al'umma da kowa zai amfana."

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, tun bayan barkewar annobar korona, China da kasashen Afirka na ci gaba da taimakon juna tare da hada hannu wajen yakar cutar.

Ya ce,"cutar korona ta zama ruwan daren da ya game duniya baki daya kuma likafar ta na ci gaba hatta a yankunan kasashen Afirka."

Zhao ya kara da cewa, "taron hadin kan wanda za a gudanar yana da muhimmanci a yayin da zai mayar da hankali wajen sabunta kyakkyawar alakar da ke tsakanin China da Afirka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel