ASUU: Dalilin da ya sa dole mu ci gaba da yajin aiki - Farfesa Ogunyemi

ASUU: Dalilin da ya sa dole mu ci gaba da yajin aiki - Farfesa Ogunyemi

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta ce ba za ta sauya ra'ayi ba kan yajin aikin da take yi wanda ya shafi daukacin jami'o'in gwamnati da ke fadin kasar.

ASUU ta ce za ta ci gaba da yajin aikin sai mama-ta-gani da ta tsunduma tun tsawon makonni 13 da suka gabata.

A ranar Talata ne kungiyar ta yanke shawarar ci gaba da yajin aikin da ta shiga da cewar har sai ta tabbatar gwamnati ta bayar da kulawa a bangaren ilimi tare da inganta jin dadin ma'aikata.

Kungiyar ta wassafa wasu dalilai da suka sanya ta ce har yanzu tana a kan bakanta na ci gaba da yajin aiki kuma babu ranar da za ta janye har sai an biya mata bukatunta.

Daga cikin dalilan da kungiyar ta bayar sun hadar da rashin biyan alawus din malamai, sai kuma rashin cika alkawalin da gwamnati ta dauka tun a yarjejeniyar da suka kulla a shekarar 2009.

Sauran dalilan sun hadar da rashin bayar da kudin farfado da jami'o'i, takaita yawan jami'o'in gwamnatin jiha da sauran ababe na inganta tsarin karantarwa.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ASUU ta ce ba za ta janye yakin aikin ba har sai gwamnatin Najeriya ta cika dukkanin yarjejeniya da suka kulla tare.

Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar mai dauke da rahoto kan yajin aikin da ya sanya wa hannu.

Shugabannin ASUU tare da shugaba Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Shugabannin ASUU tare da shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar reshen Jami'ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole, shi ne ya gabatarwa manema labarai sanarwar mai lakabin ‘Strike Bulletin 9’.

Farfesa Ogunyemi ya bayyana cewa, hanzarin tabbatar da yarjejeniyar da suka kulla tare da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009 zai haifar da cikar wasu sharuda da aka shata.

Daga cikin sharudan akwai inganta albashin malaman jami'o'i, da kuma inganta gine-gine domin farfado da martabar jami'o'in gwamnati a fadin tarayyar kasar nan.

KARANTA KUMA: Ganduje zai zaftare kashi 30% a kasafin kudin Kano na bana

Shugaban kungiyar ya jaddada cewa, mambobinsu sun dage a kan samun kyakkyawan yanayi na karantar da dalibai da kuma na aiki duk da rike albashin dubunnan malamai da gwamnatin ke ci gaba da yi.

Yayin bayar da tabbaci tare da kwantar da hankalin mambobinsu kan yankewa da rashin biyan albashi, Farfesa Ogunyemi ya ce su sha kuruminsu domin kuwa duk rintsi sai kudadensu sun fito.

Ya tabbatu a kan cewa, makasudin wannan yajin aiki shi ne tabbatar da 'yan Najeriya sun yi karatu a jami'o'i nagartattu cikin aminci ta yadda za su iya goga kafada da sa'o'insu na ketare.

A karshe Farfesa Ogunyemi ya bayyana rashin jin dadi dangane da yadda gwamnatin Najeriya ta ke yi wa yaki da annobar korona rikon sakainar kashi.

Ya hori mambobin ASUU da su kara zage dantse wajen ci gaba da bincike da wayar da kan al'umma wajen dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel