Atiku ya sake caccakar gwamnatin Buhari a kan dorawa Najeriya nauyin bashi

Atiku ya sake caccakar gwamnatin Buhari a kan dorawa Najeriya nauyin bashi

Atiku Abubakar ya ce har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta san inda ya ke mata ciwo ba sakamakon bashin da ta ke ci gaba da laftawa kanta.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake caccakar gwamnatin tarayya dangane da nauyin bashin da ta ke kara dorawa a kan kasar nan.

Yayin bayyana bacin rai dangane da nauyin bashin da ya yi wa kasar nan katutu, Atiku ya zargi gwamnatin tarayya da lalata makomar manyan gobe da za su ci gajiyar mulkin kasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, tsohon dan takarar shugabancin kasar ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta yi taka tsan-tsan da nauyin bashin da ya ke kanta.

Wazirin na Adamawa ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage kashe-kashen kudaden da ta ke yi domin sauke nauyin bashin da a yanzu ya wuce a misalta shi da katutu.

Ya yi gargadin cewa, muddin Najeriya ba ta yi wa kanta karatun ta nutsu ba ta janye jiki daga cin bashi, to akwai yiwuwar kasar za ta dulmiye a hannun masu bata bashi.

Ya ce "idan har kudaden shiga da kasar nan ta ke samu ba su yi gaggawar karuwa ba, Najeriya za ta iya fuskantar wani mummunan yanayi mai rauni tamkar yadda ta kasance ga kasar Sri Lanka da Maldives."

Tsohon mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Cable
Tsohon mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Cable
Asali: UGC

"Duk wani kudin shiga da kasar za ta samu zai sulale ne kawai wajen biyan bashi kuma a karshe ta tashi fayau babu komi a lalitar ta."

Babu shakka Atiku ya sha caccakar gwamnatin tarayya dangane da cin bashin da ta ke akai-akai. Ya yi alfahari da kasancewarsa a gwamnatin da ta sauke duk nauyin bashin da ke kan kasar nan.

Legit.ng ta ruwaito Atiku yana cewa, Mai gidansa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya biya duk bashin da ke wuyan Najeriya a lokacin da su ke mulki duk da farashin mai bai da tsada.

Atiku wanda ya koka da gwamnatin yanzu kan yawan cin bashi, ya ce idan aka ci gaba da tafiya a haka, to kuwa kwanci-tashi babu wata dama ta cin moriya da za ta rage a kasar nan.

KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamna Obaseki ya fice daga jam'iyyar APC

"Ba wai kawai mun bata damar mu ba ne, mun kuma bata damar masu tasowa ta hanyar dora musu bashin da ba su ji ba kuma ba su gani ba ballanta su ci moriyarsa," in ji shi.

A yayin haka tsohon mataimakin shugaban kasar ya nemi gwamnatin tarayya ta sanya wasu daga cikin jiragen fadar shugaban kasa a kasuwa domin rage kashe kudi wajen gyara da kula da su.

Ya ce bai dace ba a ce fadar shugaban kasar Najeriya ta na da jiragen da yawansu ya zarta na gwamnatocin kasashen da ta ke lallabawa wajen neman rancen bashi a wurinsu.

"Dole ne gwamnatin Najeriya ta gaggauta sayar da jiragen domin yin amfani da kudin wajen gina wasu muhimman wurare da za su samar da ci gaba a kasar."

"Bai kamata ba a ce darajar arzikin da ake samarwa a cikin kasar nan ya zamana yana yin kunnen doki da nauyin bashin da ke wuyan kasar nan."

"Ina sake gargadin gwamnatin Najeriya dangane da matsalar da ta ke fuskanta a yanzu, ba za mu iya ci gaba da tsayuwa da kafar mu ba ta hanyar karɓar lamuni don bunkasa tattalin arzikinmu."

"Hakan yana nufin haɗamar da muke yi a gwamnati ba ta da wani banbanci da yi wa makomar manyan gobe fashi da makami."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel