Covid-19: Mun samu gudunmuwar N1.69bn tsakanin watan Afrilu da Mayu - Gwamnatin Tarayya

Covid-19: Mun samu gudunmuwar N1.69bn tsakanin watan Afrilu da Mayu - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fayyace adadin jimillar kuɗaɗen da ta samu tsakanin watan Afrilu da Mayun shekarar da muke ciki a matsayin gudunmuwar dakile yaduwar cutar korona.

Gwamnatin ta ce tun daga ranar 1 ga Afrilu zuwa 31 ga watan Mayun 2020 ta karɓi jimillar Naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari da dubu dari shida a matsayin tallafin kawar da cutar korona.

Daraktan yada labarai da hulda da al'umma na ofishin Akanta Janar na kasa, Henshaw Ogubike, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Abuja a ranar Litinin.

Ogubike ya ce an samu wannan gudunmuwa ne ta hanyar asusun wasu manyan bankuna a Najeriya da kuma Babban Bankin Najeriya gami da asusun bai daya na TSA.

Ya yi tsokaci kan shaidar wasu asusun ajiya da gwamnatin tarayya ta buɗe kwanan nan a wasu manyan bankuna wanda ofishin Akanta Janar ya ke ajiyar gudunmuwar da aka samu a cikinsu.

Akanta Janar na kasa; Ahmed Idrid
Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Cable
Akanta Janar na kasa; Ahmed Idrid Hakkin mallakar hoto: Jaridar The Cable
Asali: Twitter

A cewar Ogubike, wannan asusun ajiya da aka buɗe kari ne a kan asusun ajiya na bai daya, domin tabbatar da ingantaccen aiki yayin gudanar da harkokin batar da kudaden.

Ya fayyace dalla-dalla jimillar Naira biliyan 1.69 da aka samu a tsakanin watanni biyu da suka gabata. Kuma tuni aka bai wa al'umma cikakken bayani game da wannan tallafin.

Ya ce daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa ranar 8 ga watan Mayu, an samu gudunmuwar naira miliyan 792.12.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Oyo ta sassauta dokar kulle, za a koma makarantu a ranar 29 ga watan Yuni

Ogubike ya kuma bayyana cewa, an karbi gudunmuwar Naira miliyan 897.64 daga ranar 9 zuwa 31 ga watan Mayu na wannan shekarar da muke ciki.

Daga cikin duk jimillar kudin, an karbi naira miliyan 710.076 ta hanyar asusun ajiya na wasu manyan bankuna a Najeriya yayin da aka karbi naira miliyan 187.56 ta hanyar asusun bai-daya.

"Daga ranar 9 zuwa 31 ga watan Mayu, an karɓi kashin Naira Miliyan 100; Naira miliyan 507.75; Naira miliyan 2.21; da kuma naira miliyan 100.11 ta hanyar wasu bankuna hudu daban-daban" in ji Ogubike.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel